Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato
Published: December 9, 2025 at 5:19 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 9, 2025

Sojoji sun kashe ’yan bindiga da suka yi wa ’yan kasuwa kwanton-bauna a Sabon Birni.

Sojoji sun kashe akalla ’yan bindiga 13 a Sabon Birni, Jihar Sakkwato, bayan sun kai dauki ga ’yan kasuwar da aka yi wa kwanton-bauna a hanyar Tarah–Karawa da safiyar Litinin.

’Yan bindigar sun tare ’yan kasuwar ne da misalin 8:00 na safe a Kwanan Akimbo, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako ta Sabon Birni, Sojojin da ke Kurawa sun yi gaggawar isa wajen, inda suka yi musayar wuta da maharan na kusan sa’a guda kafin su fatattake su.

An gano gawarwakin maharan tara a wurin, a yayin da aka gano wasu hudu a cikin daji kusa da rafin.

Sojojin sun kwato makamai da babura da dama, yayin da dukkan ’yan kasuwar aka ceto su cikin koshin lafiya, in banda fararen hula biyu da suka ji rauni.

  1. Babu asara daga bangaren sojoji, kuma mazauna Kurawa da makwabta na murnar nasarar aikin wani dan majalisar jiha, Aminu Boza, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa bincike na cigaba domin gano sauran maharan.

Harin ya faru ne kwana guda bayan kashe mutane bakwai da sace mata da dama a Gatawa da Shalla da ke yankin.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Rwanda Tana Keta Yarjejeniyar Zaman Lafiya – Tshisekedi
Next Post: Burkina Faso: Mun Kama Sojojin Najeriya da Jirgin Yaki Bisa Shigowa Ba Bisa Ka’ida Ba

Karin Labarai Masu Alaka

Dangote Ya Rage Farashin Mai A Najeriya Labarai
Rundunar Sojin KTK Ta Harba Makami Teku Afrika
Shugabannin Darikar Anglican Sun Bada Sanarwar Kafa Sabuwar Majalisa Afrika
Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
Gwamnatin Gombe Ta Aza Tubalin Gina Sakatariyar Gundumomin Cigaba (LCDAs) Labarai
Ferfesa Pantami Yasamu Tikitin Takarar Gwamnan Gombe A Jami’yar PDP Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi Labarai
  • Gwamnatin Kasar Guinea Ta Soke Wasu Jam’iyyun Siyasa Afrika
  • Sakataren Tsaron Amurka Yace Yaki Tsakanin Amurka Da Iran Zai Dauki Sabon Salon Amurka
  • Gwamnan Neja Bago Na Cin Zarafin Talakawan Da Suka Zabe Shi Labarai
  • RSF Ta Kasar Sudan, Tana Yin Garkuwa Da Mazauna A Yankin Darfur Afrika
  • Gwamnatin Kano Ta Samar Da Wasu Dabarun Inganta Tsaro Tsaro
  • Ana Kokarin Dawo Da Wutan Lantarki A Cuba Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.