Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe Afrika

Hukumar NAPTIP Ta Kubutar Da Yara 11 Daga Hannun Masu Safara Mutane
Published: December 15, 2025 at 2:16 PM | By: Mahmud Kwari | Updated: December 16, 2025

Hukumar NAPTIP, dake yaki da safara da fataucin bil’adama a Najeriya, ta dakile yunkurin wasu bata gari na safarar wasu yara su 11 ‘yan asalin jihar Jigawa a yankin arewa maso yammacin Najeriya. Hukumar tace tuni ta mika yaran da Jami’an ta suka kubutar ga majalisar karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Kwamandan hukumar a jihar ta Jigawa Abdulkadir Turajo ya fada yayin taron masu ruwa da tsaki a Dutse, shalkwatar jihar cewa, jami’an hukumar ta NAPTIP sunyi nasarar kubutar da yaran a birnin Lokoja na jihar Kogi yayin da ake kokarin kai su wani wurin da ba’a bayyana ba.

Yace yaran wadanda dukkanin su maza ne zalla, ‘yan shekaru 7 zuwa 15, an kwaso su ne daga kauyukan Tsaba da Kunkurawa da kuma Tsabare a karamar hukumar Ringim ta jihar ta Jigawa.

Kwamandan hukumar ta NAPTIP a Jigawa ya yabawa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar da kuma hadin kan da suka baiwa hukumar wajen sada yaran da iyayen su cikin hanzari.

Batun safarar yara kanana, galibi daga yankin arewaci zuwa kudancin Najeriya wani kalubale da hukumomin kasar ba su kai ga magance shi ba, duk da cewa, iyaye yara a yankin na arewacin Najeriya sun dade suna kokawa dangane da wannan matsala.

A shekarun baya baya nan, wannan matsala tayi kamari a Jihar Kano, jiha mafi yawan Jama’a a kasar, al’amarin daya kai ga hukumomin jihar sun kafa wani kwamitin bincike mai karfi domin lalubo hanyoyin dakile wannan matsala da galibi aka gano cewa, ana boye yaran ne jihohin Enugu da Abia bayan an yi safarar su daga Kano.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina
Next Post: Rikici Ya Barke A Kano Bayan Kashe Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Ladani

Karin Labarai Masu Alaka

Kimanin Mutane 200 Ne Suka A Mutu A Wani Harin Jirgin Yakin Sojin Najeriya Afrika
An Yankewa Prime Ministan Kasar Tunisiya Hukuncin Shekaru 24 A Gidan Yari Afrika
Jami’an Diflomasiyyar Iran Dana Amurka Sun Tattauna A Kasar Oman Afrika
Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon Labarai
Amurka Zata Hana Kwankwaso Shiga Kasar Amurka
Yau Lahadi Ake Gudanar Da Zabe A Kasar Myanmar Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS
  • Hukumar ‘Yan Sanda Tayi Yarjejeniya Da ‘Yan Takara A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Kebbi Ta Samu Tankokin Yaki Tsaro
  • Majalisa A Kasar Somaliya Ta Amince Da Sauya Tsarin Mulkin Kasar Afrika
  • Ruwan Sama Yayi Ajalin Daruruwan Mutane A Afirka Ta Kudu Afrika
  • Hukumomin Kasar China Suna Goyon Bayan Somaliya Labarai
  • Dakarun Tsaron Ruwan Amurka Sunfara Killace Hanyoyi Amurka
  • Wani Bayahude Ya Harbe Bafalatsine Dan Shekaru 16 Tsaro
  • Marc Brys: “Eto’o Baiyi Adalci Ga Onana, Da Vincent, Ba” Wasanni
  • Gwamnatin Tinubu Zata Samar Da Wutan Solar A Jami’ar ADUST Wudil Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.