Gwamnatin jihar Gombe ta musanta zargin da ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi cewa, ana cin zarafi ko wulaƙanta waɗanda suka soki gwamnatin jahar.
Wata sanarwar da kakakin gwamnatin jahar Ismaila Uba Misilli ya fitar da yammacin Juma’a, ta ce babu ƙamshin gaskiya a zargin da ƙungiyar ta yi bayan wani faifan bidiyo ya nuna ɗaya daga cikin hadiman gwamnan jihar yana marin Kansilar gundumar Shamaki.

A sanarwar, Misilli ya ce bai kamata a riƙa alaƙanta lamarin da gwamnatin jihar ba, har ma ya yi gargaɗi game da saka siyasa kuma ya nesanta hannun wani jami’in gwamnati ko gwamnatin jhar a ciki.
Sanarwar ta ce babu wanda ya fi ƙarfin doka, kuma tuni aka fara ɗaukar matakan bincike dan ɗaukar mataki kan lamarin da ya sha suka daga al’umma.
Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa a guji alaƙanta lamarin da gwamna ko gwamnatin jihar, tana mai cewa Gwamna Inuwa Yahaya baya goyon saɓa doka ko cin mutuncin wani.
A yanzu dai ƙungiyoyin da al’umma na jiran ganin matakin da gwamnatin za ta ɗauka a kan wanda ake zargin.


