Amurka ta fara janye wasu ma’aikata daga sansanonin sojanta a yankin gabas ta tsakiya, a bayan da wani babban jami’in Iran ya gargadi makwabtansu cewa Iran zata kai hari kan sansanonin Amurka idan har aka kai mata hari.
A yayin da hukumomi a birnin Teheran ke kokarin kwantar da wutar tarzoma mafi muni tun bayan juyin juya halin Islama da aka yi, Teheran tana son yin hannunka mai sanda ma shugaba Donald Trump da barazanarsa ta tsoma baki domin goyon bayan masu zanga zangar kin jinin gwamnati.
Wani jami’in Amurka da bai so a fadi sunansa ba yace Amurka tana kwashe ma’aikata daga wasu muhimman sansanoninta a saboda karuwar tankiya.
Wani jami’in soja a kasar yammaci yace a bisa dukkan alamu Amurka ta yanke shawarar zata kai ma kasar Iran farmaki, amma kuma yace irin wannan dabi’a gwamnatin Trump ta saba nunawa na haddasa yanayin kokwanto a kan zata kai ne ko ba zata kai harin ba.
Amma kuma a fadarsa ta White House, shugaba Trump ya nuna alamun kamar yana jira ya ga yadda lamarin zai wakana ne, trump yace wata majiya mai tushe ta fada masa cewa yawan kashe kashe ya ragu, kuma babu wani shirin da aka yi a yanzu na zartas da hukumcin kisa a kan mutane masu yawa.
Wasu jami’an Turai guda biyu ma sun ce watakila nan da sa’o’i 24 Amurka zata kai hari a kan kasar Iran haka ma wani jami’in gwamnatin bani Isra’ila yace da ala mun shugaba Trump ya yanke shawarar zai tsoma hannu a Iran, amma ba a san irin farmakin da zai kai ko kuma lokacin kaiwa ba.


