Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe
Published: March 8, 2026 at 4:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙungiyar Mata Manoma a Najeriya, wato WOFAN, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Salamatu Garba, ta raba buhunan shinkafa dubu biyar ga mata a jihar Gombe domin tallafa musu wajen inganta rayuwar iyalansu, a wani shiri da aka gudanar domin tunawa da Ranar Mata ta Duniya.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da rabon tallafin, Shugaban WOFAN a Jihar Gombe, Usman Rayyanu Dabai, ya bayyana cewa shirin ya shafi mata a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar da suka haɗa da Gombe, Akko, Yamaltu Deba, Kwami da Dukku.

Ya ce an shirya wannan tallafi ne a wani ɓangare na bikin Ranar Mata ta Duniya, domin ƙarfafa mata da kuma taimaka musu su tallafa wa iyalansu, musamman mazajensu, wajen tafiyar da al’amuran gida.

Rayyanu Dabai ya kuma yi kira ga mata a faɗin Jihar Gombe da su ci gaba da bai wa mazajensu haɗin kai a harkokin gida, domin ƙarfafa zaman lafiya da kyakkyawar rayuwar aure.

A nasu jawaban yayin karɓar tallafin, wasu daga cikin sarakunan gargajiya da suka haɗa da Banban Hakimin Gombe, Alhaji Bappah Ibrahim, Hakimin Bokna, Alhaji Abubakar Usman Deba, da Lamidon Akko, Alhaji Umaru Muhammadu Atiku, sun yaba wa Hajiya Salamatu Garba bisa wannan karamci da ta nuna wa al’ummar Jihar Gombe.

Sarakunan gargajiyar sun kuma buƙaci mata a jihar da su zauna lafiya da mazajensu tare da riƙa ba su goyon baya, domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kan iyalai.

An gudanar da bikin ƙaddamar da rabon tallafin ne a Makarantar Firamare ta Orji Estate da ke Gombe, inda wakilan mata daga kowace ƙaramar hukuma da abin ya shafa suka halarta domin karɓar nasu kaso na tallafin.

Afrika, Labarai, Najeriya, Nishadi, Rumbun Hotuna

Post navigation

Previous Post: Ambaliyar Ruwa Yayi Ajalin Mutane A Nairobi
Next Post: Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini

Karin Labarai Masu Alaka

3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
Tawagar Shirya Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Ta Ziyarci Masarautun Jihar Labarai
Majalisar Dottijan Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Na’ura Labarai
Mawakiyar Amurka Cardi B. Ta Cashe A Saudi Araibiya Nishadi
Shugaban Hukumar NAHCON Ya Yabawa ‘Yan Jarida Kiwon Lafiya
Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
  • Masu Ruwa Da Tsaki Sun Buƙaci Ƙarin Tallafi Ga Iyaye Mata Masu Shayarwa A Gombe Afrika
  • Lauyoyi Sun Gurfanar Da Wani A Kotu Bisa Fasa Korin Kiyashi A Kenya Afrika
  • Najeriya Zata Kara Mai Da Take Hakowa Afrika
  • Tinubu Na Kokarin Rage Tsadar Sufuri Ta Hanyar Shirin CNG Afrika
  • Shugaba Trump Ya Yabawa Iran Bisa Bude Mashigar Hormuz Amurka
  • Kano Pillars Ta Doke Ikorodu City Wasanni
  • Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.