Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Amurka Ta Jefa Makamin Tomahawk A Makarantar Yara Mata
Published: March 10, 2026 at 4:30 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wasu sabbin hotunan bidiyo sun nuna abinda wasu kwararru suka bayyana a zaman wani makami mai linzami samfurin Tomahawk na Amurka yana fadawa dab da wata makarantar yara mata inda aka kashe yara fiye da 165 a farkon yakin da aka kai kan Iran.

Wannan yana zuwa ne a yayin da ake kara samun shaidar cewa lallai Amurka ce ta kai harin da yayi sanadiyyar kashe wadannan dalibai mata yara a makarantarsu dake Minab a lardin Hormozgan na kudancin kasar.

Wani jami’in Amurka dake da masaniya game da tattaunawar dake wakana a tsakanin shugabannin Amurka ya fadawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa a bisa dukkan alamu Amurka ce ta kai harin da ya fada kan makarantar.

Sabbin hotunan bidiyon da aka dauka a ranar da aka kai hari kan makarantar, wata kungiyar bincike mai suna Bellingcat ce ta fara nazarinsa, kuma a ranar lahadi kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya yada shi. Hotunan sun nuna makami mai linzami yana fadawa a kan makarantar.

Kamfanin dillancin labaran AP ma yayi nazarin hoton bidiyon ya kuma samu shaidar cewa lallai an dauka ne daga wani gini dake gefen wannan makaranta.

Wani mai bincike na Bellingcat, Trevor Ball, ya ce wannan makami mai linzami lallai samfurin Tomahawk ne, wanda Amurka ce kadai aka san tana da shi a wannan yakin. Wannan kuma ita ce shaidar farko ta irin makamin da aka yi amfani da shi a kan makarantar ta yara dalibai mata.

Afrika, Amurka, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Rahoton Leken Asiri Yanuna Cewa Harin Amurka Bazai Samar Da Shugabanci A Iran Ba
Next Post: Shugaba Putin Ya Bukaci Kawo Karshen Yaki Da Iran

Karin Labarai Masu Alaka

Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika
Iran Ta Bukaci Duniya Ta Shirya Domin Fuskantar Tsadan Mai Amurka
Angano Gawar Wani Dan Myanmar A Arewacin New York Afrika
An Kashe Mayakan Sakai 67 A Pakistan Sauran Duniya
Kungiyar Cigaban Al’ummar Tangale Tace Bata Goyon Bayan Kai Ziyara Wa Gwamnan Gombe Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Burkina Faso: Mun Kama Sojojin Najeriya da Jirgin Yaki Bisa Shigowa Ba Bisa Ka’ida Ba Afrika
  • Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato Afrika
  • Tawagar IMF Tana Kasar Kenya Domin Tattauna Bada Lamuni Labarai
  • Jihar Gombe Ta Karbi Bakuncin Taron Tsaro Tsakanin DIG Da Masu Ruwa Da Tsaki Afrika
  • Bola Ahmed Tinubu Ya Soke Bashin Da Gwamnati Take Bin NNPC Najeriya
  • Gwamnatin Kasar Benin Ta Nemi ‘Yan Kasa Su Kwantar Da Hankali Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Laraba 11.19.2025 Rediyo
  • ‘Yan Tawaye A Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Kasar Ghana Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.