Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gangamin Wayar Da Kai Don Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Jihar Gombe
Published: November 25, 2025 at 9:26 PM | By: Bala Hassan | Updated: November 26, 2025

Uwargidan Gwamnan jihar Gombe, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, ce ta kaddamar da gangamin kwanaki goma sha shidan domin fafutukar kawo karshen cin zarafin jinsi a cikin al’umma.

An gudanar da taron kaddamarwar a Filin wasa na Pantami Gombe, inda taken wannan shekarar ya kasance: “Mu hadu guri ɗaya don kawo ƙarshen cin zarafin mata da ’yan mata ta hanyar amfani da kafafen sadarwar zamani.”

A yayin kaddamarwar, a karakashin ma’aikatar harkokin Mata da cigaban al’umma ta jihar Gombe, Uwargidan Gwamnan ta jaddada bukatar haɗin kai tsakanin al’umma da hukumomi, domin dakile dukkan nau’o’in cin zarafi da ke afkawa mata da ’yan mata, musamman barazanar da suke fuskanta ta kafafen intanet.

Ta kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su ƙara jajircewa wajen kare mutunci, tsaro, da damar amfani da kafafen zamani ga mata da ’yan mata a Gombe da ma kasa baki ɗaya.

Tawagar wacce ta kunshi matan shugabanin kananan hukumomi, kwamishinoni dasauran Mata masu rike da mukamai daban-daban a jihar, da zummar kawo karshen cin zarafin jinsi a tsakanin al’umma.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Za’a Fuskanci Bala’in Yunwa A Najeriya
Next Post: Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL

Karin Labarai Masu Alaka

Shahararren Dan Dambe Anthony Joshua Yayi Hatsarin Mota A Jihar Ogun Labarai
2025 Ta Bar Baya Da Abubuwa Masu Ban Al’ajabi, 2026 Barka Da Zuwa! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar-Ta-Baci A Fannin Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tinubu: Zamu Kara Kyautata Samar Da Kayan Aiki Ga Jami’an Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Zelensky Na Buƙatar Ganawa Da Trump Domin Cimma Matsaya Kan Batutuwa Masu Sarƙaƙiya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Trump: Zamu Kawo Zaman Lafiya A Fadin Duniya Amurka
  • Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Borno Tsaro
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Anyi Rashin Mutane Da Yawa Yayinda Bom Ya Fashe Ana Sallar Magariba Maiduguri Labarai
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Tura Sojoji Benin Labarai
  • Shugaban Ƙasar Koriya Ta Arewa Ya Halarci Gwajin Makami Mai Linzamin Kasar Labarai
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Laraba 11.19.2025 Rediyo
  • Mawakiyar Amurka Cardi B. Ta Cashe A Saudi Araibiya Nishadi
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.