Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Peter Obi Ya Gayyaci Gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Kan Yazo Su Hada Kai Su Gyara Nijeriya. Labarai
  • Tawagar Masu Yi Wa Maniyyata Hidima Za Ta Tashi Zuwa Saudiyya Afrika
  • ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
  • Za A Cigaba Da Tattaunawa Domin Kawo Karshen Yakin Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi
Published: April 25, 2026 at 6:39 PM | By: Bala Hassan

Barayin Waya sun yanke yatsun hannun guda biyu da gefen Kunne da fiskan wacce Suka qwace wa waya.

Daga Ahmad Muhammad, Bauchi
Wassu barayin Masu qwacen waya,sun yanke yatsun hannun guda biyu da gefen Kunne da fiskan Wata daliba Mai Suna Maryam Yakeem, Daliba ‘yar aji 200 a fannin Ilimin Halittu, a Jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU), Gadau da ke jihar Bauchi  Arewa maso gabas a Najeriya.

Lamarin ya faru ne a cikin Garin Gadau hedikwatar Qaramar Hukumar Itas Gadau a wajen harabar jami’ar, yayin da kuma shugabannin Jami’ar suke tabbatar da tsaron ma’aikata da dalibai a harabar Jami’ar.

Wasu mutane daga yankin sun ce masu satar wayar, su huɗu ne, sun bi matar suka nemi qwace wayarta da qarfi.

Yayin da take ƙoƙarin tserewa sai ɗaya daga cikin masu laifin ya zare wuqarsa mai kaifi ya yanke yatsun hannunta biyu yayin da ya kwace wayar daga hannunta da ƙarfi.

Barayin sun yi mata mummunan rauni a fuska da kuma wani ɓangare na kunnenta. a ƙoƙarin qwace wayarta.

Mazauna garin sun nuna damuwa game da lamarin, suna kira ga hukumomin tsaro da su tashi tsaye don ganin an gano masu laifin kuma a kama su ba tare da ɓata lokaci ba.

Mazauna garin sun nuna fushinsu kan yadda masu laifin ke addabar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a cikin ‘yan kwanakin nan, wanda hakan ya sa mutanen Suna zaune cikin fargabar.
Ganin cewa garin ɗalibai ne, suna buƙatar ƙarin jami’an tsaro don kare mazauna yankin.

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da abkuwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya shaida wa manema labarai a Bauchi cewa wadanda ake zargin sun yi wa matar mummunan rauni, yayin da suke qoqarin qwace wayarta da qarfi.

Nafiu ya ce ‘Yan sanda sunyi himma wajen gano wadanda ake zargin, da nufin a qwato wayan da suka qwace da kuma gurfanar da su a gaban kotu bayan bincike don a musu hukunci.

Hakazalika, Mallam Auwal Hassan Jami’in Hulɗa da Jama’a na Jami’ar Sa’adu Zungur, Bauchi ya bayyana cewa Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar (SAZU), ta ce lamarin da ya faru kwanan nan ya shafi ɗaya daga cikin ɗalibanta, Maryam Yakeem, ɗaliba mai aji 200 a fannin Ilimin Halittu,

Yace an ruwaito cewa wasu mutane da ba a san ko su waye ba ne suka kai mata hari, waɗanda ake zargin masu satar waya ne.

Awwal a cikin sanarwar ya ce “Wannan mummunan lamari ya faru ne a wajen muhallin Jami’ar, sabanin wasu rahotannin da ke yawo a wasu kafofin watsa labarai na yanar gizo da ke nuna cewa harin ya faru ne a cikin harabar Jami’ar. Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar tana son ta bayyana cewa wannan iqirarin ƙarya ne kuma ba ya nuna gaskiyar lamarin”.

Mataimakiyar Shugabar Jami’ar, Farfesa Fatimah Tahir, ta sake nanata cewa Jami’ar ta ci gaba da ba da fifiko ga tsaro da tsaron ɗalibanta da ma’aikatanta a cikin harabar jami’o’inta guda uku.

Ta hanyar ci gaba da haɗin gwiwa da tsarin tsaro na cikin gida da hukumomin da suka dace, Jami’ar ta sami gagarumar nasara, ba tare da rahoton wani lamari na rashin tsaro a cikin harabar jami’ar ba.

Idan “Za a tuna cewa Mataimakiyar Shugaban Jami’a a wasu lokutan ta ziyarci Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jiha don ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da haɓaka tallafin tsaro ga al’ummar Jami’ar.

“Hukumar Jami’ar ta nuna damuwa kan ayyukan wasu kafofin yaxa labarai na kan yanar gizo suna yaɗa bayanai marasa tabbas da ba gaskiya.
waɗanda za su iya haifar da firgici da tashin hankali . Irin wannan ɗabi’a ta gaza da ɗabi’a da ƙwarewa da ake tsammani a aikin jarida.” Dangane da lamarin, da ya faru, Shugaban Jami’ar ta Tura Babban Jami’in Tsaro na Jami’ar da kuma babban Jami’in da ke Kula da walwalar xalibai, suka ziyarci wanda abin ya shafa nan take a asibiti don tabbatar da cewa ta sami isasshen kulawar likita.

Muna farin cikin bayar da rahoton cewa yanayin lafiyarta ya infants tana samun sauqi. Mataimakiyar Shugaban Jami’ar, ta nuna tausayawa ga ɗalibar da abin ya shafa. Jami’ar za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin dukkan ɗalibai. Hukumar tana kira da a kwantar da hankali tsakanin ɗalibai, ma’aikata, da jama’a baki ɗaya, kuma tana tabbatar da cewa ana ɗaukar duk matakan da suka dace don tabbatar da ci gaba da tsaron mutane Jami’ar, a ciki da wajen harabar jami’ar.

Har zuwa lokacin da aka kammala rahoton, matar tana karɓar maganina wani wuri a garin Gadaubkafin a tura ta zuwa Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya dake Azare

Labarai

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Najeriya Ta Samar Da Wuta Mai Aiki Da Hasken Rana A Jami’ar ADUSTECH

Karin Labarai Masu Alaka

Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka Afrika
Za A Rantsar Da Mainasara Kogo A Matsayin Shugaban Kundin Da’ar Ma’aikata Labarai
Masu Goyon Bayan Palasdinawa Sunyi Gangamin Zanga Zanga A Australia Labarai
Maharan Bindiga Sun Kashe Mutane 12 Masu Hakar Ma’adanai A Jihar Filato Labarai
Amurka Da Isra’ila Sunkai Hari Kan Iran Amurka
Sojojin Amurka Sun Kutsa Cikin Kasar Iran Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi
  • Gwamnatin Najeriya Ta Samar Da Wuta Mai Aiki Da Hasken Rana A Jami’ar ADUSTECH
  • Hukumar EFCC Ta Kama Dan Kasuwa A Kamaru
  • Al’ummar Jihar Nasarawa Suna Cecekuce Bisa Tsaida Aliyu Wadada Takarar Gwamna
  • Gwamnatin Tarayya Tayi Baje Kolin Nasarorin Tinubu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yan Fashi Sun Shiga Gidan Alex Iwobi A Ingila Wasanni
  • Sojojin Amurka Sun Kutsa Cikin Kasar Iran Labarai
  • Yakin Gabas Ta Tsakiya Ya Kawo Cikas Ga Cinikin Nama A Kenya Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Talata 11.18.2025 Rediyo
  • Salmanu: Ci Gaban Wikki Tourist FC Shine A Gaba Na Wasanni
  • Rasha Da Ukraine Sun Cigaba Da Yakar Juna Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tura Mutane 386 Gidan Yari Afrika
  • Dalibai Sun Koma Makarantu A Wasu Jihohin Najeriya Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.