Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis Afrika
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
  • Tinubu Ya Sake Fasalin Rundunar Sojin Ƙasa Domin Inganta Tsaro Afrika

Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Published: July 27, 2026 at 7:22 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Dakarun Operation Fansan Yamma sun ceto fararen hula 48 da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara bayan sun dakile wani hari da ‘yan ta’adda suka kai da sanyin safiyar Asabar a ƙauyen Magami da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda.

A wata sanarwa da Mai Bayar da Bayanai na Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya fitar, ya ce dakarun Sector 2 sun samu kiran gaggawa cewa wasu ‘yan ta’adda kimanin mutum 40 da ke kan babura sun mamaye ƙauyen Magami.

Da isar dakarun wurin, sun fafata da ‘yan ta’addan a wani mummunan artabu. Sakamakon matsin lambar da sojojin suka yi musu, ‘yan ta’addan sun yi watsi da mutanen da suka sace tare da tserewa cikin daji.

Sanarwar ta ce farar hula guda ta rasa ranta yayin harin, yayin da wasu biyu suka samu raunukan harbin bindiga, kuma an garzaya da su zuwa Babban Asibitin Kaura Namoda domin samun kulawar likita.

Bayan kammala aikin ceton, dakarun sun ƙaddamar da sintiri mai ƙarfi a yankin Magami da dazukan da ke kewaye domin tabbatar da tsaro da hana sake kai hare-hare.

Rundunar ta yaba da jarumtaka da ƙwarewar dakarun wajen gudanar da wannan aiki cikin nasara, tare da sake jaddada aniyarta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin Arewa maso Yamma.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis

Karin Labarai Masu Alaka

Afirka Ta Kudu Zata Fuskanci Koma Baya A Bangaren Samar Da Ayyukanyi Afrika
Kwamitin Aikin Hajjin Najeriya Ya Shigar Da Korafi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ganduje Ne Yasa Aka Kama Ni Inji Muhuyi Magaji Najeriya
Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika
Ga Fili Ga Doki Dambarwar APC Da ADC Najeriya
Iran Zata Shigar Da Lebanon Cikin Cimma Yarjejeniya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
  • NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
  • Farashin Mai Ya Cigaba Da Tashi Afrika
  • Matatar Man Dangote Ta Samu Tagomashi Daga Abokan Hulda Najeriya
  • Ma’aikatan Tattara Kudin Haraji Sunyi Rikici Da Masu Babura A Bauchi Najeriya
  • Zanga-Zangar Adawa Da Harin Amurka Da Isra’ila Ya Zamo Tarzoma A Pakistani Afrika
  • Fafaroma Leo Yayi Allah Wadai Bisa Karuwar Yake Yaken Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Tinubu Ya Sayi Fom Din Takarar Shugaban Kasa Afrika
  • Ukraine Tana Cigaba Da Tattaunawa Da Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Kasar Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.