Kwamitin 3G Taskforce ya ci gaba da aikin dasa bishiyoyi a gefen hanyoyin da ake ci gaba da aikinsu da kuma wadanda aka kammala a cikin birnin Gombe, inda aka gudanar da sabon aikin dasa bishiyoyi a kan sabuwar hanyar Gombe zuwa Bauchi.
Aikin ya shafi hanyar da ta taso daga Hedikwatar ‘Yan Sanda, ta bi ta Kwalejin Ilimi ta Tarayya, FCET, zuwa hanyar Mechanics Village, wadda aka mayar da ita tagwayen hanya.
Da yake jawabi jim kadan bayan kammala aikin, Shugaban Kwamitin kuma Mai Tula, Dakta Abubakar Atare Buba, ya ce shirin ya yi daidai da hangen nesan Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, na mayar da jihar cikin yanayi mai yawan ciyayi da bishiyoyi, tare da dakile matsalolin kwararowar hamada da zaizayar kasa.
Dakta Abubakar ya yi kira ga al’umma da su rungumi al’adar dasa bishiyoyi a yankunansu, tare da rokon mahukuntan FCET, tashar motoci ta Dankwanbo da kamfanin Gombe Line da su taimaka wajen kare bishiyoyin da aka dasa har zuwa lokacin da za su girma.
Shugaban Kwamitin ya yaba wa mambobin kwamitin da sauran jami’an da suka halarci aikin, bisa jajircewarsu da sadaukarwar da suka nuna wajen ganin an cimma nasarar shirin.
Ya bayyana cewa an sayo tare da kula da tsirrai da aka dasa domin bai wa kwamitin damar cimma adadin bishiyoyin da ya tsara dasawa.
Haka kuma, ya yabawa ofishin ACReSAL na jihar Gombe bisa goyon baya da kuma hadin gwiwar da yake bayarwa wajen aiwatar da shirin.

Wasu daga cikin masu wucewa da aka zanta da su, ciki har da Zainabu Mohammed da Musa Kanawa Yamaltu, sun bayyana shirin dasa bishiyoyin a matsayin abin da ya zo a kan lokaci, suna cewa zai taimaka wajen samar da muhalli mai tsafta, lafiya da kuma dacewa da rayuwar al’umma.


