Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya karɓi Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Gida na jihar, Alhaji Adamu Dishi Kupto, a wata ziyarar sanayya da ya kai hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar.
Ziyarar ta kasance wata dama ta ƙarfafa haɗin gwiwa da zurfafa hulɗa tsakanin hukumomin tsaro da ma’aikatar, domin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kare lafiyar al’umma a faɗin Jihar Gombe.
Da yake jawabi yayin ziyarar, CP Umar Ahmed Chuso ya nuna godiyarsa ga Kwamishinan bisa ziyarar, tare da jaddada aniyar rundunar ‘yan sandan na ci gaba da aiki kafada-da-kafada da ma’aikatar da sauran masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da laifuka da magance matsalolin tsaro.
Ya kuma jaddada muhimmancin musayar bayanan sirri, gaggauta mayar da martani ga barazanar tsaro, haɗa kai da al’umma da kuma gudanar da ayyukan tsaro cikin tsari guda domin tunkarar sabbin ƙalubalen tsaro.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Gida, Alhaji Adamu Dishi Kufto, ya yaba da ƙoƙarin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Ya yi alkawarin ci gaba da ba rundunar ‘yan sandan da sauran hukumomin tsaro cikakken goyon baya da haɗin kai, domin cimma burin samar da jihar Gombe mai aminci da kwanciyar hankali.
Ziyarar ta ƙare da sake jaddada ƙudurin ɓangarorin biyu na ƙarfafa haɗin gwiwa da kuma samar da hanyoyin tunkarar sabbin ƙalubalen tsaro a Jihar Gombe.


