Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa Afrika
  • Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki Afrika
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika

Matatar Man Dangote Zata Wadatar Da Najeriya Da Makota
Published: December 1, 2025 at 9:45 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

A Najeriya kamfanin tace man fetur na Dangote, ya fada yau Litinin yana iya samarda man fetur lita bilyan daya da rabi ako wani wata. Daga nan ya gayyaci hukumomin kula da samar  da man fetur a kasar su ziyarci kamfanin don su gasgata, bayanda sashen ya wallafa alkaluma da suke nuna cewa, matatar man fetur yana samar da kashi daya cikin uku na wannan adadi.

Maganganu da ake yi cewa matatun mai da suke kasar basa iya samar da wadataccen mai da Najeriya take bukata, yana daga cikin dalilan da suka sa gwamnati ta dakatar da hana shigo da tataccen mai daga ketare.

Hukumomin kasar dake sa ido sun ce Najeriya tana bukatar litan mai milyann 55 a kowace rana, ko litan mai bilyan daya da digo 67 ako wani wata.

Kamfanin yace Mai da suke samarwa a Dangote “a shirye su ke kuma suna da karfin” samarda tataccen mai lita bilyan daya da rabi a cikin watan nan na Disamba, da kuma watan Janairu, daga bisani kuma zai iya samarda litan mai bilyan daya da digo bakwai a watan Febwairu har sai yadda hali yayi.

Kamfanin matatar mai na Dangoten yace domin kaucewa duk wata kumbiya kumbiya ya gayyaci hukumomin kasar dake sa ido kan samar da man fetur su taho matatar Man daga yau daya ga watan Disamba, su wallafa alkaluman abunda matattar Man take sarrafawa ako wace rana kuma ta fadawa duniya.

Ahalinda ake ciki kuma, tattalin arzikin Najeriya ya habaka da kusan kashi hudu a cikin wata uku daga Yuli zuwa Satumba, a bangarorin da basu shafi Mai ba.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Jihohin Arewaci Sun Kafa Asusun Yaki Da Ta’addanci
Next Post: Ministan Tsaron Najeriya Badaru Yayi Murabus

Karin Labarai Masu Alaka

Ribadu: Najeriya Ce Kasa Daya Tilo Da Ke Tabbatar Da Demokraɗiyya A Sahel Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tawagar Masu Yi Wa Maniyyata Hidima Za Ta Tashi Zuwa Saudiyya Afrika
Shahararren Dan Dambe Anthony Joshua Yayi Hatsarin Mota A Jihar Ogun Labarai
Zamu Hana Wasu ‘Yan-Najeriya Visa Shiga Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Bukaci Matasa Su Taka Gagarumar Rawa Wajen Gina Zaman Lafiya A Arewa Maso Gabas Afrika
Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa
  • Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rikicin Siyasa A Jihar Rivers Sakamakon Ayyana Fubara A Matsayin Shugaban APC Siyasa
  • Shugaban Ƙasar China Zai Karbi Bakwancin Shugaban Koriya Ta Kudu Afrika
  • Zamu Hada Kai Mu Yaki Cutar Shan’inna (Polio) Labarai
  • Amurka Ta Kwace Jirgin Mai Mallakar Rasha Amurka
  • Wasu Mutane 15 Sun Rasa Rayukan Su A Gabashin Kwango Afrika
  • Gwamnatin Somaliya Da MDD Sun Bayyana Cewa Kimanin Mutane Miliyan Shida Da Rabi Suna Fuskantar Barazanar Yunwa Labarai
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika
  • Jihar Gombe Ta Karbi Bakuncin Taron Tsaro Tsakanin DIG Da Masu Ruwa Da Tsaki Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.