Gidauniyar Ci gaban Al’umma ta Misilli ta shigar da ƙarin yara 60 cikin makarantun firamare a Jihar Gombe, lamarin da ya sa adadin yaran da suka amfana da tallafin ilimi na gidauniyar tun bayan kafuwarta ya kai 210.
Mai kula da ayyukan gidauniyar, Yusuf Hamza, ne ya bayyana hakan a yayin bikin karɓar rukunin yara na huɗu da gidauniyar ta ɗauka, wanda aka gudanar a gidan wanda ya kafa gidauniyar, Alhaji Isma’il Uba Misilli, da ke unguwar Dawaki a Gombe.
Yusuf Hamza ya ce an kafa gidauniyar ne a shekarar 2018, domin mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya da kuma ci gaban al’umma, inda ya bayyana ilimi a matsayin babban ɓangaren ayyukan gidauniyar.
Ya ce gidauniyar ta tallafa wa yara daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar shigar da su makarantu, ba su tallafin karatu da kuma fom ɗin JAMB, tare da haɗin gwiwa da shirin AGILE wajen samar da kayan karatu.
Wakilin Kwamishinan Ilimi na jihar Gombe, Alhaji Abdullahi Abubakar, tare da wasu jami’an gwamnati, sun yaba wa gidauniyar bisa yadda take taimaka wa gwamnati wajen bunƙasa fannin ilimi.
Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Barrister Sani A. A. Haruna; Kwamishinan Kuɗi, Alhaji Muhammad Gambo Magaji; Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Farfesa Abubakar Bappah Garkuwa; da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Gombe North, Ali Baba Manu, sun yi kira ga daidaikun mutane da ƙungiyoyi da su tallafa wa gidauniyar domin ta faɗaɗa ayyukanta.
A nasa ɓangaren, wakilin shirin AGILE na Jihar Gombe, Alhaji Jabiru Kilawa, ya yaba da haɗin gwiwar da ake samu, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta damar samun ingantaccen ilimi, musamman ga ’yan mata.
Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Gombe, Hamza Baba, ya ce samun ilimi haƙƙi ne na kowane yaro, yana mai bayyana cewa gwamnatin jihar, ta hannun Hukumar SUBEB, ta shigar da dubban yaran da ba sa zuwa makaranta cikin tsarin karatu.
Shi ma mai ba Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, shawara kan harkokin Almajirai kuma dattijo mai kishin al’umma, Alhaji Yaya Hammari, ya yaba wa gidauniyar bisa ci gaba da tallafa wa marasa ƙarfi da sauran masu buƙatar taimako a cikin al’umma.
Da yake jawabi, wanda ya kafa gidauniyar, Alhaji Isma’il Uba Misilli, ya ce an kafa shirin ne domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen samar da dama ga yara marasa galihu, marayu da sauran masu rauni a cikin al’umma.
A yayin bikin, an bai wa wasu daga cikin ɗaliban da suka nuna ƙwazo kekuna, jakunkunan makaranta da littattafan karatu.
Haka kuma, gidauniyar ta bai wa mata da tsofaffi 200 tallafin ƙarfafa tattalin arziƙi, inda kowannensu ya samu naira dubu goma.
Gidauniyar ta ce za ta ci gaba da ayyukan tallafa wa ilimi da sauran shirye-shiryen ci gaban al’umma domin taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi a Jihar Gombe.


