Kasar Afirka ta kudu ta sanar da samun allurar rigakafi na farko cikin shekaru 20 kan cutar boro, (foot and mouth disease) a turance, yayin da take neman bunkasa sarrafa maganin rigakafin a cikin gida, don tunkarar barkewar annobar mafi muni a shekaru masu yawa.
Cutar boro, cuta ce da ake saurin dauka, Wadda kuma Shanu zasu iya kamuwa da ita.
Tana sa kuraje a baki da kofato masu radadi da ciwo. Duk da cewa bata fiye jawo mutuwar shanun ba, amma tana dakile amfanin da ake samu daga dabbobin, kama da haihuwa ko samun madara.
Rigakafin, wadda hukumar binciken aikin noma ta Afirka ta Kudu ta samar, wani bangare ne na kudurin da kasar ke da shi na yiwa kashi 80 cikin 100 na shanun ta da suka kai kimanin miliyan 12 allura.
Hukumar zata rika samar da allurai 20,000 kowanne mako, daga watan Maris na wannan shekarar, har ta kara wa’adin zuwa 200,000 a shekarar 2027.


