Shugaban Kungiyar Kawancen Kasashen Yankin Sahel yace tilas a biyo bayan kafa rundunar sojojin hadin guiwa ta kasashen da kaddamar da gagarumin farmaki a kan ‘yan ta’adda cikin ‘yan kwanakin da suke tafe a yankin da ta’addanci yayi tsanani.
Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore, bayyi karin bayani akan wannan furuci nasa ba, a bayan da aka ayyana shi a zaman shugaban Kungiyar Kawancen Kasashen Yankin Sahel, kungiyar da kasashe 3 dake cikinta suka balle daga cikin kungiyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, ko CDEAO, a wannan shekarar.
Kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar sun fi fuskantar ta’addanci a yankin bakin iyakokinsu a yayin da wannan yanki na Sahel dake kudu da hamadar Sahara ya zamo inda aka fi ganin ayyukan ‘yan ta’adda masu alaka da al Qaida da kungiyar Daesh, watau ISIS.
Shugabannin kasashen uku sun cimma daidaituwa a taron kolinsu na ranar talata, a kan bunkasa hadin kan tsaro da na tattalin arziki, kuma a karshen makon nan, kasashen uku sun kaddanar da sabuwar bataliya ta hadin guiwa wadda zata yaki ‘yan ta’adda na yankin sannan ana sa ran zata kumshi dakaru dubu 5.
Shugaban Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani, yace kungiyarsu ta samu nasarar kawo karshen sojojin mamaya a cikin kasashensu, bisa dukkan alamu gugar zana yake yi kan shawarar da kasashen suka yanke na korar sojojin faransa da Amurka daga cikin kasashensu.
Tchiani ya kara da cewa babu wata kasa ko kungiya da a yanzu zata gaya musu abinda ya kamata su yi.
Yanzu dai kasashen uku, sun karkata ga kasare Rasha domin tallafa musu wajen ayyukan tsaron yankinsu.


