Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya
Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya samu muƙamin Kodinetan Tattara Masu Ruwa da Tsaki na Yankin Arewa Maso Gabas a sabon Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasar Najeriya na Jam’iyyar APC na shekarar 2027. An bayyana naɗin Gwamna Inuwa Yahaya ne cikin jerin sunayen mambobin kwamitin da aka fitar ranar Asabar, 22 ga…

