Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar APM A Bauchi Ya Bada Gudummawar Naira Miliyan ₦21 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Bara Da Shira
Published: June 23, 2026 at 7:40 PM | By: Bala Hassan

Dan takarar gwamna na jam’iyyar APM ya bayar da gudummawar Naira miliyan ₦21 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Bara,da wadanda guguwar iska ta afkawa a Shira

Daga Ahmad Muhammad, Bauchi

Dan takarar gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) a jihar Bauchi, Dakta Yakubu Adamu, ya bayar da gudummawar Naira miliyan ₦21 don tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a yankin karamar hukumar Kirfi da kuma wadanda guguwar iska ta shafa a yankin karamar hukumar Shira.

Adamu ya bayar da gudummawar ne lokacin da ya kai ziyara a lokuta dabam-dabam ga al’ummomin da abin ya shafa, inda ya nuna tausayawa da jimaminsa ga wadanda bala’in ya abka musu da wadanda suka rasa rayukansu.

A yankin Bara da ke karamar hukumar Kirfi inda ambaliyar ruwa ta faru, sakamakon ruwan sama mai karfi da yake fitowa daga gabas zuwa garin ya yi sanadiyyar mutuwar wata tsohuwa Mai Suna, Aishatu Sagir, da jikarta Mai Suna Rahama Sagir.

Ambaliyar ta lalata gidaje sama da 360 da dama ta Kayar katanga da dama, ta lalata gonaki, ta kashe dabbobi, sannan ta bar daruruwan mazauna yankin sun yi hijira suna kwana a cikin masallatai da makarantu.

A lokacin ziyarar jaje ga al’ummomin da abin ya shafa, Yakubu Adamu ya bayyana rasuwar iyalan biyu na al’ummar a matsayin abin tausayi, sannan ya sanar da bayar da gudummawar ₦10,000,000 ga wadanda abin ya shafa da kuma ₦1,000,000 ga iyalan da suka rasu.

Ya yi addu’ar Allah ya sauwaka musu wahalhalun da suke sha, ya kuma saka musu da alheri da hakurinsu, ya kuma gafarta wa wadanda suka rasu.

Hakimin Bara Alhaji Muhammad Abdullahi Bara, ya nuna godiyarsa ga dan takarar gwamna na APM a madadin al’ummar yankin

Ya bayyana cewa taimakon da ya Bayar zai taimaka wajen rage wa wadanda abin ya shafa wajen rage musu asarar da suka yi.

Mazauna Bara sun yaba wa Yakubu Adamu saboda ziyarar, sun bayyana taimakon da ya bayar cikin gaggawa a matsayin alama na nuna tausayi,da kuma nuna kyakykyawan jagoranci mai kyau a lokacin da ake nema ”

A yankin karamar hukumar Shira, dan takarar gwamna na APM, Dr. Yakubu Adamu, ya bayar da gudummawar agajin ₦10,000,000 miliyan don tallafawa iyalai da guguwar iska mai karfi ta lalata wa gidaje da kadarori a yankin.

Wannan tallafin an yi shi ne ga al’ummomin da abin ya shafa, ciki har da garuwan Dango, Disina, da Zubo, inda iyalai da yawa suka shiga cikin damuwa bayan bala’in guguwar ta yi musu barna mai yawa ga matsugunan su da hanyoyin rayuwa.

Dr. Yakubu Adamu, ya bayyana kaduwarsa, da firgici kuma ya baiwa al’ummomin da abin ya shafa hakuri kuma ya roke su da su dauke shi a matsayin kaddara daga Allah.

Adamu ya bayyana cewa shugabanci ba wai kawai a baki bane, har ma game da nuna damuwa ta gaske, daukar mataki, da kuma amsa bukatun mutane lokacin da suka fi bukatar hakan.

Ya ce bala’o’i kamar guguwar iska da ambaliyar ruwa, abubuwane dake jefa Al’umma cikin matsaloli da wahala mai yawa, sai ya yi kira da a tallafawa wadanda abin ya shafa don rage musu radadi.

Adamu ya tabbatar wa Iyalan da abin ya shafa ba su kaɗai ba ne, kuma ya bayyana cewa tallafin kuɗi an yi shi ne don samar da agajin gaggawa da kuma taimaka wa waɗanda abin ya shafa su fara aikin murmurewa daga barnar da guguwar iska ta haifar.

Ya yi kira ga hukumomi, ƙungiyoyi da kuma mutane masu kyakkyawar niyya da su ba da tallafi ga waɗanda wadannan bala’o’i suka shafa, yana mai lura da cewa ƙoƙarin haɗin gwiwa yana da mahimmanci wajen sake gina al’ummomin da abin ya shafa.

Mazauna al’ummomin da abin ya shafa sun yaba da wannan taimako, sun bayyana shi a matsayin taimakone daya zo a lokacin da aka fi bukatarsa kuma alama ce ta nuna tausayawa ga mutanen da ke cikin wahala.

kuma sun tabbatar da cewa taimakon zai taimaka sosai wajen rage musu radadi da kuma taimaka musu su gyara gidajensu da rayuwarsu.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Idan Allah Yasa Muka Kafa Gwamnati Zamu Kyautata Wa Ma’aikata Yakubu Adamu Dan Takarar Kujeran Gwamnan Bauchi
Next Post: NAHCON Ta Yaba da Nasarar Hajjin 2026, Ta Fara Shirin Hajjin Shekara Mai Zuwa

Karin Labarai Masu Alaka

Jihar Filato Ta Rufe Makarantu Don Dakile Yaduwar Diphtheria Afrika
Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka
Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Ummulkhairi Afrika
Shugaba Tinubu Ya Ware Kudade Domin Bunkasa Rayuwar ‘Yan Najeriya Afrika
‘Yan Bindiga Sun Karya Alkawarin Dakatar Da Kai Hare Hare A Najeriya Labarai
Aisha Buhari Ta Bayyana Irin Kalubalen Da Ta Fiskanta Sakamakon Biyewa Jita-Jita Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF Wasanni
  • Da Alamu Ronaldo Zai Buga Dukkan Wasanni Da Gasar Kofin Duniya A 2026 Wasanni
  • Isra’ila Takai Hare Hare Birnin Tehran Afrika
  • Akwai Bukatar Nazari Game Da Dangantakar Iran Da Kasashen Gulf Amurka
  • Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar Labarai
  • An Kaddamar Da Rigakafin Cutar HIV AIDS A Kasar Zimbabwe Kimiya
  • Aikin Layin Dogon Kasar Uganda Zai Hade Kasar Da Tanzania Da Kwango Kimiya
  • An Bude Gasar Bauchi Annual International Polo 2026 Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.