Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

FRSC Gombe: Hatsarin Mota Ya Yayi Ajalin Mutane 38 Ya Jikkata Fiye Da 218 A Wata Ɗaya
Published: January 18, 2026 at 9:13 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 18, 2026

Mutane 38 Sun Mutu, 218 Sun Jikkata a Wata Ɗaya Sakamakon Hatsarurrukan Mota.

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa, FRSC, reshen jihar Gombe, ta ce ta samu rahoton hatsarurrukan mota 38 tsakanin ranar 15 ga Disamba, 2025, zuwa 15 ga Janairu, 2026.

A cewar hukumar, hatsarurrukan sun shafi motoci 74 tare da shafar mutane 345, Daga cikin adadin, mutane 218 sun samu raunuka daban-daban, yayin da mutane 38 suka rasa rayukansu.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Route Commander Janet Kassa, ta fitar a madadin Kwamandan Sashen jihar, Samson Kaura, kuma aka bai wa manema labarai a Gombe.

Sanarwar ta danganta mafi yawan hatsarurrukan da kuskuren ɗan Adam da kuma matsalolin injunan mota, ciki har da ɗaukar kaya ko fasinjoji fiye da ƙima, gudu ba bisa ƙa’ida ba, gajiyar direba, da tuƙi a ƙarƙashin tasirin ƙwayoyi.

Sauran abubuwan da suka taimaka wajen faruwar hatsarurrukan sun haɗa da lalacewar tayoyi, matsalar birki, da rashin isasshen haske, kayan tsaro, ko kuma alamomin hanya.

Hukumar ta yi kira ga direbobi da su guji tuƙin ganganci, amfani da wayar hannu yayin tuƙi, tafiya saɓanin hanya, da duk wani abu da ke iya daukar hankalinsu daga kan hanya.

Da take jaddada cewa kiyaye lafiya nauyi ne na kowa da kowa, Janet Kassa ta ce dole ne direbobi su daina tuƙi cikin sakaci.

Hukumar ta kuma tabbatar da ƙudirin ta na rage yawan hatsarurrukan mota zuwa mafi ƙarancin mataki.

A cewar sanarwar, “FRSC na ci gaba da aiwatar da ayyukanta na tabbatar da hanyoyi masu aminci a jihar Gombe ta hanyar sintiri na yau da kullum, cire cikas a kan hanya, ayyukan ceto, da wayar da kan jama’a a tashoshin mota da wuraren ibada.”

Hukumar ta lura cewa ƙarshen shekara da farkon sabuwar shekara na daga cikin lokutan da ake samun yawaitar zirga-zirga sakamakon ƙaruwa a harkokin jama’a, lamarin da galibi ke zuwa da barazana ga rayuka da kuma tattalin arziki.

Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: An Kashe Mutane 7 A Unguwar Dorayi Dake Kano
Next Post: Gwamnatin Najeriya Ta Taya Super Eagles Murnar Lashe Tagulla A Gasar AFCON

Karin Labarai Masu Alaka

Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas Najeriya
‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayin Shanu Tsaro
Jamhuriyar Nijar Ta Fitar Da Doka Domin Kare ‘Yancin ‘Yan Kasar Tsaro
Lauya Bala: Tabbas Kotu Zata Soke Zaben Shugaban PDP, Turaki Najeriya
Rikici Ya Barke A Kano Bayan Kashe Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Ladani Najeriya
Kasashen Cambvodia Da Thailand Sun Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shirin Kwace Iyakar Greenland Da Shugaba Trump Yakeyi Yabawa Kasashen Turai Mamaki Amurka
  • Amurka Tana Cigaba Da Kare Jami’in Da Ya Kashe Ba Amurke Amurka
  • Rundunar Tsaron Haɗin Gwiwa Ta Arewa Maso Gabas Ta Kashe Fiye Da ‘Yan Ta’adda 438 Labarai
  • Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Shugaban Amurka Donald Trump Ya Jadda da Kudirinsa Da Kwace Iyakar Greenland Amurka
  • Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai
  • Amurka Ta Kai ‘Yan Cirani Kamaru Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.