Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnatin Sham Tace Harin Kurdawa Ya Hallaka Sojojin Kasar
Published: January 21, 2026 at 9:36 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin kasar Sham ta ce harin da kungiyar ‘yan tawayen kurdawa ta SDF ta kai wa dakarun ta da jiragen drone ya yi sanadiyar hallaka sojoji 7 ranar laraba duk da kungiyar SDF din sun musanta hakan.

Wannan abu na barazanar kawo koma baya ga yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu suka kulla, bayan da suka shafe kwanaki suna gwabza kazamin fada.

Sojin Sham sun ce, wannan harin da aka kai yayin da dakarun nasu ke neman killace wani sansanin sojoji da aka kame mai dauke da bama bamai, tunzura ce me hadari.

Kungiyar ta SDF ta ce bata kai hari ba, ta ce an samu fashewar bama bamai ne lokacin da sojojin Sham ke kokarin matsar su. Ta kuma zargi sojojin na Sham da karya alkawarin yarjejeniyar zaman lafiya hanyar kai hare-hare a wurare da dama.

Bayan shafe kwanaki tana ci gaba da samun nasara, gwamnatin Sham ta ce ran Talata, ta cimma fahimta tsakanin ta da dakarun SDF, don yarda da yarjejeniyar tsagaita wuta na kwana hudu, kuma su yarda su kasance karkashin mulkin gwamnatin, ko kuma a ci gaba da kai musu farmaki a birane biyu da suka rage musu da suke rike da madafun iko.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Harin Jirgi Maras Matuki Ya Hallaka Mutane A Sudan
Next Post: ‘Yan Kasar Venuzuela Zasu Fara Komawa Gida

Karin Labarai Masu Alaka

Jirgi Marar Matuka Yayi Luguden Wutan A Abu Dhabi Afrika
Iran Ta Kama Wasu ‘Yan Leken Asiri Afrika
Trump Yace Amurka Ta Kai Hare-Hare Masu Yawa Akan ‘Yan Ta’adda A Najeriya Amurka
Amurka Ta Girke Jirage Marasa Matuki Tare Da Sojoji A Najeriya Afrika
Yajin Aikin Ma’aikatan Lafiya Na Shafar Harkokin Jinya A Asibitoci Kiwon Lafiya
‘Yan Tawayen Houthi Sunkai Hari Isra’ila Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ana Cigaba Da Yaki Tsakanin Amurka Da Isra’ila Da Kasar Iran Afrika
  • NNPC Da Wasu Kamfanoni Sunyi Yarjejeniyar Iskar Gas Najeriya
  • Hukumar NAPTIP Ta Kubutar Da Yara 11 Daga Hannun Masu Safara Mutane Labarai
  • Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
  • Dangote Ya Rage Farashin Mai A Najeriya Labarai
  • Harkar Zirga Zirgar Jiragen Sama Ya Bunkasa A Kenya Afrika
  • Isra’ila Tace Bazata Sake Kai Hari Kan Cibiyar Gas Ta Iran Ba Afrika
  • Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan Hakkokin Tsofin Ma’aikata 800 Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.