Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Jami’an Askarawa A Zamfara Sun Kama Na’urorin Fashewa Da Makudan Kuɗaɗe
Published: April 16, 2026 at 8:59 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jami’an Rundunar Karewa Al’umma a jihar Zamfara, da aka fi sani da “Askarawa”, sun kama wasu na’urorin fashewa, makudan kuɗaɗe, da sauran kayan tallafi da ake zargin za’a kaiwa ’yan bindiga a ƙauyen Bindin da ke Ƙaramar Hukumar Maru.

Kwamandan rundunar CPG na jihar, AIG Shehu Muhammad Dalijan (mai ritaya), ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargi tare da kayayyakin da aka ƙwato ga manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Gusau.

Ya ce wannan nasara ta biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa wata mota mai ɗauke da kaya ta tashi daga Danhasiya Plaza da ke Gusau zuwa ƙauyen Bindin, yankin da ake zargin yana ƙarƙashin ikon ’yan bindiga.

A cewarsa, jami’an sun tare motar mai lamba KMC 120-XR, inda suka kama direban tare da wasu mutane shida kuma ayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da kuɗi Naira miliyan 13,352,500, abubuwan fashewa 98 na na’urorin gargajiya (IEDs) da ake zargin dynamite ne, na’urorin tayar da fashewa guda 25, babura sababbi guda uku, wayoyin Android, sigari, ’ya’yan itacen tuffa, jarkoki huɗu na dizal, jarkoki uku na man ja, da kuma kayan haƙa kamar felaye da cokula.

Dalijan ya ce za a miƙa waɗanda aka kama tare da kayayyakin ga ’yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

A cikin bayaninsa, direban motar, Abubakar Abdullahi Dangulbi, ya ce wani mai suna Aliyu Labaran ne ya ɗauke shi aiki domin kai kuɗin ga wani Alhaji Abubakar Bindin daga hannun wani Nasiru Dan Zuru (wanda ke tsere), yayin da aka ce na’urorin fashewar na wani Jamilu Lingyado ne a ƙauyen Bindin, Sai kuma yace bai san abin da ke cikin kayan ba, yana mai jaddada cewa shi aikin kai saƙo kawai aka ba shi.

“Ban san abin da ke cikin kayan ba. An ba ni aikin kai su ne kawai ga masu su a Bindin,” in ji shi.

Dalijan ya yi gargaɗi cewa matsalar tsaro da ke addabar jihar Zamfara na samun ƙarfi ne daga masu haɗin gwiwa da ke samar wa ’yan bindiga kayan aiki, bayanan sirri da sauran tallafi, ya kuma jaddada cewa irin waɗannan na’urorin fashewa na iya jawo asarar rayuka masu yawa ga fararen hula da jami’an tsaro.

Ya ƙara da cewa rundunar CPG za ta ci gaba da ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu aikata laifuka, tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar.

Haka kuma, ya yaba wa gwamnatin jihar Zamfara kan tallafin kayan aiki da take bayarwa, yana mai cewa za a yi amfani da su yadda ya kamata wajen yaƙi da ’yan bindiga.

Wannan nasara ta ƙara nuna damuwa a tsakanin masana harkar tsaro cewa matsalar ’yan bindiga a Zamfara na ƙara samun goyon baya ta hanyar tsare-tsaren samar da kayayyaki masu ƙarfi, lamarin da ke buƙatar ƙarin tsauraran matakan sa ido da kuma katse hanyoyin samar da irin waɗannan kayayyaki.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Jami’yar ADC A Najeriya Ta Kori Nafiu Bala
Next Post: Shugaba Tinubu Yace Bazai Bawa ‘Yan Najeriya Kunya Ba

Karin Labarai Masu Alaka

Akwai Doka Mai Tsanani Wajen Mallakar Bindiga A Kasashen Yammacin Turai Labarai
Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika
An Gudanar Da Idin Karamar Sallah A Birnin Niamey Labarai
Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Zata Karbi ‘Yan Gudun Hijirar Da Amurka Ta kora Afrika
Gwamnatin Filato Ta Gurfanar Da Maharan Rukuba A Kotu Afrika
Hukumomi A Kasar Syri Lanka Suna Kokarin Fidda Jirgin Yakin Iran Daga Kasar Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Take Hakkin Dan Adam Zai Haifar Da Juyin Juya Hali A Najeriya Najeriya
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika
  • Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
  • Gwamnan Jihar Filato Na Shirin Komawa APC Siyasa
  • Putin, Sakon Sabuwar Shekara Ya Jinjinawa Dakarun Rasha Da Suke Yaki A Ukraine Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Spain Zata Bada Diyya Ga Iyalen Wadanda Da Suka Rasu A Hatsarin Jirgin Kasa Labarai
  • Gwamnatin Tinubu Zata Gyara Hanyar Akwanga Zuwa Jos Labarai
  • Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.