Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Masu Kare Hakkin ‘Yan Gudun Hijira A Amurka Sun Mika Koke
Published: January 23, 2026 at 8:32 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Masu rajin kare hakkin ‘yan gudun hijira sun mika takaddar koke zuwa kotu don dakatar da kudurin gwamnatin shugaba Donald Trump na soke damar samun mafaka, da bada izinin zama da aka bawa dubbannan ‘yan kasar Ethiopia da ke zaune Amurka.

Wasu ‘yan kasar Ethiopia 3, tare da kungiyar masu rajin kare hakki ta mazauna ‘yan Afirka sun gabatar da kara a wata babbar Kotun kasa da ke birnin Boston na jihar Massachusettes, ranar Alhamis cewa Ma’aikatar Tsaron Cikin gida ta Amurka tana neman salwantarwa da mutane fiye da dubu biyar damar da suke da shi na samun mafaka ta wucin gadi ba bisa ka’ida ba. Sun ce ma’aikatar na nema ta sa mutanen su rasa mafakar su bayan 13 ga watan Fabrairu.

Sun ce duk da kasar ta Ethiopia har yanzu tana cikin halin dake barazana ga rayukan mutane, sakatariyar tsaron cikin gida Kristi Noem ta soke mafakar da Amurka ta bawa ‘yan Ethiopian ba bisa ka’ida ba, kuma ta basu wa’adin kwana 60 kacal.

Wannan na daga cikin korafe korafe na kwanan nan da ake kaiwa gaban kotu don kalubalantar yunkurin gwamnatin Trump, na dakile mafaka da mutane ke da shi, da ake yiwa ‘yan asalin wasu kasashe da dama.

A tsarin dokar kasa, ana bawa mutanen da kasashen su ke fama da gurbacewar yanayi, yaki, ko wasu abubuwan da ka iya kawo barazana ga rayuwar al’umma. Ana bawa ‘yan gudun hijira da suka cancanta takardun damar samun aiki, kuma a basu mafaka ta wucin gadi, da zata tsare su daga fuskantar kora daga kasa.

An sha kawowa kotu korafi don kalubalantar neman korar mutane da suka fito daga wasu kasashe da suka hada da Sham, Venezuela, Haiti, Nicaragua, da kuma Sudan ta Kudu, inda ake samu kotu ta dakatar ko ta hana gwamnatin ta Trump soke takardun zama na mutanen.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana
Next Post: An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi

Karin Labarai Masu Alaka

Za’a Saka Tarihin Trump A Manhajar Makarantu Don Jajircewasa Da Kwazo Amurka
Maganganun Jami’an Shige Da Fice Dana Shugaban Kasa Trump Suna Cin Karo Da Juna Amurka
Kotun Amurka Ta Soke Harajin Fito Da Shugaba Trump Ya Kakabawa Kayan Kasashen Waje Amurka
Farashin Zinari Yayi Tashin Gwauron Zabi Amurka
Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka
Kasar Amurka Takara Saka Takunkumi Akan Kasar Venezuela Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Madrid, Arsenal Da Chelsea Sun Fara Zaurancen Dan-Wasa Kenan Yildiz Wasanni
  • Amurka Tace Zata Gama Yakin Iran Cikin Makonni Afrika
  • Hamas Ta Kwance Damara Afrika
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa
  • Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Ya Bar PDP Ya Koma APC Labarai
  • Kasashen Da Suke Kawance Da Amurka Sun Juyawa Trump Baya Afrika
  • ‘Yan Jarida Sunyi Mummunan Hatsari A Bauchi Labarai
  • Kasar Amurka Da Rasha Zasu Kawo Karshen Tsagaita Nukiliya Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.