Shugaban Afirka ta tsakiya Faustin Toudera yayi kira ga Rasha ta taimakawa kasar sa ta fuskar makamashi saboda kalubale da kasar take fuskanta ta wannan fanni.
Shugaba Toudera wadda yayi wannan kira a ranar Alhamis, ya kuma godewa Rasha, a fara ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu a Moscow, yace Rasha ta taka muhimmiyar rawa ta fuskar tsaro a kasar wadda ya bada damar a gudanar da zaben kasar da aka yi bada jumawan nan ba, da ya bashi nasara na wani wa’adi na shekaru bakwai. Yace Rasha tana da kwarewa ta fuskar makamashi.
Kasashen yammacin duniya suna nuna damuwa saboda ganin karin rawar da Rasha take takawa a wasu sassan Afirka, wadda hakan koma baya ne ga muradun Faransa da Amurka. Rundunar Afirka da Rasha wacce ta gaji Kungiyar sojojin haya na Rasha da ake kira Wagner, tana aiki a kasashen Afirka da dama da suka hada da Mali, da Equatorial Guinea, da Afirka ta tsakiya.
Shugaban Rasha Vladimiri Putin yace kasashen biyu suna da damar kara karfafa dangantaka tare da da aiki da juna ta fuskar makashi, noma, da kuma samarda ababen more rayuwa.


