Babban hafsan sojin Uganda Muhoozi Kainerugaba yace yana addu’ar Allah ya kashe shugaban ‘yan hamayyar kasar Bobi Wine, ya kuma bashi sa’o’i 48 ya mika kansa ga ‘Yan sanda, bayan zaben shugaban kasar mai cike da rikici.
Tsohon mawakin zamani Bobi Wine, yace ya tsere daga gidansa, sa’o’i gabannin a ayyana dadadden shugaban kasar Yuweri Museveni a zaman wanda ya lashe zaben kasar da aka yi cikin makon jiya.
Bobi Wine wanda ya shine na biyu, yayi zargin an tafka magudi a zaben. Ya fidda bayanai daban daban tun ranar Asabar, daga maboyarsa.
Kainerugaba, wanda dan Yuweri Museveni ne, kuma ana rade-raden cewa shine shugaban kasar yake so ya gaje shi, yayi ta barazana kan Bobi Wine a bayanai da yayi ta wallafa a daren ranar Litinin, a dandalin X, inda yake kiran Bobi Wine da wani suna na batanci wai “Kabobi.”
A wani sakon, Kainerugaba, ya kira jam’iyyar Bobi Wine NUP watau National Unity Platform Party da turanci cewa, “mun kashe ‘yan ta’adda 22 na jam’iyyar NUP tun a makon jiya, ina addu’ar na 23 zai kasance Kabobi.
Dama ana fargabar cewa irin tarzomar da ta biyo bayan zaben Tanzania, inda daruruwan rayuka ko dubbai suka halaka, za’a ta auku a Uganda, hakan bai tabbata ba.


