Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Tsohon Lauyan Amurka Jack Smith Ya Fadi Maganganu Game Da Donald Trump
Published: January 23, 2026 at 2:20 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon lauyan Amurka Jack Smith wanda bai sami nasarar ci gaba da gurfanar da Trump gaban shari’a ba saboda zaben sa da aka yi, ya gayawa kwamitin majaisar wakilan Amurka ranar Alhamis cewa, Trump ya “nemi hanyoyin yin tazarce,” duk da cewa ya fadi zabe a shekara ta 2020, yayinda yake amsa zargen zargen da ‘yan Republican suke yi masa game da binciken da ya gudanar kan Donald Trump.

Jack Smith ya amsa tambayoyi daga kwamitin kula da harkokin shari’a karkashin ‘Yan Republican, kan kararraki biyu da ya shigar gaban kotu yana tuhumar Trump da laifin neman ci gaba da mulki alhali ya fadi zabe, da kuma murdiya kan muhimman kasidun gwamnati kana daga bisani yayi watsi da su bayan Trump ya sami nasara a zaben da aka yi bara.

Wannan shine karo na farko da Amurkawa za su ji daga bakin Smith kai tsaye kan wadannan shari’u biyu da suka mamaye harkokin Trump bayan ya sauka daga mulki.

“An tuhumi Trump ne saboda shaida ta tabbatar da gangan, ya karya dokokin da yasha rantsuwa zai kare,” Smith ya gayawa wakilan majalisa dake kwamitin. Ya ci gaba da cewa idan aka buka ce ni in jagoaranci shar’iar tsohon shugaban Amurka da shaidar da ake ita, zan yi haka ba tare da bata lokaci, ko la’akari daga wace jam’iyya ya fito ba.

Lauya Smith yace yana jin ma’aikatar shari’a ta Amurka zata shigar da kara a gaban kotu akansa, sakamkon binicken da yayi kan shugaba Trump.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Shugaban Rasha Yafara Ganawa Da Jakadun Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Ukraine
Next Post: Gwamnan Jihar Kano Ya Fice Daga Jam’iyar NNPP

Karin Labarai Masu Alaka

Yaki Ta Sararin Samaniya Ya Cigaba Tsakanin Amurka, Isra’ila Da Iran Afrika
Trump: Isra’ila Ta Daina Kai Hari Ga Duk Cibiyar Iskar Gas Afrika
Sakataren Tsaron Amurka Yace Yaki Tsakanin Amurka Da Iran Zai Dauki Sabon Salon Amurka
Amurka Da Tarayyar Turai Sun Fidda Sanarwa Afrika
Hamas Ta Kwance Damara Afrika
Afirka Ta Kudu Tace Bazata Yanke Alaka Da Iran Ba Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Yanayin Yunwa Yana Kara Ta’azarra A Somaliya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Yusuf Gawuna Ya Koma Jam’iyar ADC Afrika
  • Wani Abu Ya Fashe A Ofishin Jakadancin Amurka Dake Kasar Norway Afrika
  • Take Hakkin Dan Adam Zai Haifar Da Juyin Juya Hali A Najeriya Najeriya
  • Sudan Takai Hari Kasar Chadi Da Jirgi Marar Matuki Afrika
  • Donald Trump Yace Basu Cimma Matsaya Da Benjamin Natanyahu Ba Afrika
  • Dalibai Sun Koma Makarantu A Wasu Jihohin Najeriya Najeriya
  • Kungiyar Enyimba: Bamu Da Niyyar Rage Albashin ‘Yan-Wasa Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.