Wani babban jami’in Iran ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Alhamis cewa matsayar da Amurka ta gabatar na tsaida yakin da ake tafkawa tsakanin sun so kan su da yawa, kuma babu adalci a cikin sa. Jami’in ya jaddada cewa har yanzu akwai kofar tattaunarwa sulhu ta diplomasiyya, duk da cewa a yanzu babu wani shiri na hakika kan tattaunawar wanzar da zaman lafiya.
Jami’in yace manyan jami’an Iran da kuma wakilin jagoran koli na kasar sun yi nazarin kudurin da aka gabatarwa fadar gwamnatin Tehran ta hannun Pakistan sosai a ranar Laraba.
Kudurin da Amurka ta bayar a cewar jami’in bai kunshi mafi karancin abubuwan da ake bukata don cimma nasara ba, kuma a tsarin sa Amurka da Isra’ila kadai zai yiwa amfani, inda yace idan fadar Washington zata fuskanci abinda ya dace za’a iya samun budewar hanyar warware rikicin.


