Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta
Published: March 23, 2026 at 1:56 PM | By: Bala Hassan

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Bauchi ta yi Allah wadai da mummunan hari da wasu jami’an ‘yan sanda suka kai wa ma’aikatan gidan rediyon Albarka a Bununu, Tabawa Balewa LG, Jihar Bauchi a lokacin bikin Sallah.

“Wannan mummunan aiki na ta’addanci babban take hakkin dan adam ne, kuma ya zamo karan tsaye ga ‘yancin manema labarai, da kuma nuna rashin bin doka da oda daga jami’an da ake sa ran za su kare lafiya da dukiyoyin al’uma, ba cutar da ‘yan ƙasa ba.

Abin damuwa ne musamman ganin irin wannan rashin da’a yana faruwa a daidai lokacin da NUJ ke ƙara himma wajen fafutukar neman ƙwarewa da riƙon amana tsakanin hukumomin tsaro. ” inji ta.

Takardar dauke da sa hanun Sakataren ta na Jiha Isah Garba Gadau, an wallafa a ranar Litinin 23/03/2026
ta buƙaci Kwamishinan ‘Yan Sanda, na Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya gaggauta bincika lamarin tare da hukunta duk jami’in da aka sa me shi na da hannu a wannan mummunan aiki.

Bugu da ƙari, Ƙungiyar ta ce dole ne, ba tare da ɓata lokaci ba, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta ɗauki alhakin biyan duk wani kuɗaɗen magani da wanda abin ya shafa ya kashe.

Idan kuma ba a cika waɗannan buƙatun ba, Ƙungiyar za ta kira taron gaggawa don yanke shawara kan mataki na gaba.

Ta kuma ƙara kira ga dukkan kafafen yaɗa labarai a jihar da su kasance cikin shiri kuma su jira ƙarin umarni domin Ƙungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an yi adalci kuma an tabbatar da tsaron ‘yan jarida da kare musu mutuncinsu.

Ƙungiyar NUJ ba za ta lamunci cin zarafi, ko cin mutumcin ga ‘yan jarida a kowane hali ba.

In za’a iya tunawa a ranar lahadi 22 ga watan Maris 2026, kafan sadarwar zamani da kuma manyan gidajen jarida su ka wallafa hoton wani dan Jarida mai suna Muhammad Adamu ma’aikaci a gidan Rediyo Albarka da ke jihar Bauchi Arewa maso gabas a Najeriya cikin jini bayan da suka samu sa in sa tsakaninsa da Jami’in Dan Sanda mai kula da Division na Bununu da ke Karamar hukumar Tafawa Balewa Bauchi.

A cewar dan Jaridar ya je aiki ne dan dauko rahoton bukukuwar Sallah da ake yi a wannan gari ta Bununu, yayin da yazu shiga wajan sai DPOn ‘yan sanda na Bununu SP Jamilu Kabir da yaransa suka lakkada masa dukan kawo wuka har suka masa rauni a kansa ba tare da karya wata doka ba.

A bangaren ta rundunan ‘Yan Sanda na Jihar ta bakin Jami’in hulda da jama’anta SP Nafi’u Habib, ya ce sun samu labarin afkuwar lamarin suna kan bincike domin bin kadin duk mai gaskiya ta re da daukan matakin da ya dace a hukumance.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Ana Kokarin Dawo Da Wutan Lantarki A Cuba
Next Post: Shugaba Trump Yace Akwai Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Iran

Karin Labarai Masu Alaka

Rasha Ta Yiwa Amurka Tayin Daina Bada Bayanan Sirri Afrika
Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
Jam’iyyar APC Ta Rantsar Da Sabbin Shugabanni a Jihar Neja Labarai
Jama’a A Yankin Gulf Sun Bukaci Dakatar Da Hare Hare Daga Washington Afrika
Hukumar NAHCON Ta Kamallah Shirye Shiryen Hajjin 2026 A Kasar Saudiya Labarai
An Gargaɗi Mazauna Maiduguri Su Guji Yaɗa Labaran Ƙarya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kungiyar HPV A Jihar Gombe Ta Jagoranci Yaki Da Karuwar Cutar Daji
  • Majalisar Dokokin Kamaru Ta Amince Da Wasu Sauye Sauye
  • Jami’an Tsaro Suna Farautar Wasu ‘Yan Ta’adda A Najeriya
  • Rasha Takai Hari Ukraine Da Jirgi Marar Matuki
  • Isra’ila Zata Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Wasu Mutane 15 Sun Rasa Rayukan Su A Gabashin Kwango Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar-Ta-Baci A Fannin Tsaro Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Tura Rundunar Tsaron Sham Zuwa Kakarshin Ikon Kurdawa Labarai
  • Wani Jirgin Kasa Yayi Hatsari A Kudancin Spain Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar Labarai
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa Afrika
  • Fitaccen Dan Jarida a Sokoto Surajo Dalhatu Sifawa Ya Rasu Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.