Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Sauya Sunan Lafarge Africa Zuwa HBM Nigeria Plc Zai Samar Da Cigaba – Sarkin Fulanin Gombe
Published: June 22, 2026 at 7:14 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Kamfanin Kasuwar Hannayen Jari ta Najeriya (NGX Group), Alhaji Dakta Umaru Kwairanga, Sarkin Fulanin Gombe, ya taya shugabanni, ma’aikata da masu ruwa da tsaki na HBM Nigeria Plc murnar sauya sunan kamfanin daga Lafarge Africa Plc zuwa HBM Nigeria Plc.

Kwairanga ya bayyana hakan ne a wajen bikin ƙaddamar da sabon sunan kamfanin da aka gudanar a birnin Lagos ranar Lahadi, 21 ga Yuni, 2026.

Ya bayyana kamfanin a matsayin ɗaya daga cikin tsofaffi kuma fitattun kamfanonin masana’antu a Najeriya, yana mai cewa tarihin kamfanin ya samo asali tun shekarar 1960 lokacin da aka fara samar da siminti a masana’antar Ewekoro.

A cewarsa, kamfanin ya kasance abin koyi wajen gudanar da harkokin kasuwanci cikin nasara, kyakkyawar alaƙa da al’ummomin da yake aiki a cikinsu, da kuma aiwatar da manufofin ci gaba mai ɗorewa.

Shugaban na NGX ya ce HBM Nigeria Plc na daga cikin kamfanonin da aka jera a kasuwar hannayen jari ta Najeriya tsawon shekaru masu yawa, kuma tana cikin rukunin Premium Board, wanda ake warewa ga manyan kamfanoni masu ƙarfi a fannin kasuwanci da cikakken bin ƙa’idojin shugabanci nagari.

Ya ƙara da cewa kamfanin ya cika tare da zarce dukkan sharuddan da ake buƙata domin kasancewa a wannan matsayi, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa a kasuwar hannayen jari ta ƙasar.

Kwairanga ya bayyana cewa sauye-sauyen mallaka da sunan kamfanin da aka yi a baya sun kasance tare da inganta ayyukansa da gudummawar da yake bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.

Ya ce yana sa ran sabon sauyin da aka samu bayan Kamfanin Huaxin Building Materials Group ya zama babban mai hannun jari zai haifar da ƙarin bunƙasar kasuwanci, ƙaruwa a yawan kuɗaɗen shiga, riba mai ɗorewa da kuma ƙarin anfani ga masu hannun jari da sauran masu ruwa da tsaki.

Dangane da ci gaban masana’antu, shugaban na NGX ya yaba da kudurin kamfanin na faɗaɗa ƙarfin samar da siminti a Kamfanin Ashaka Cement da ke Jihar Gombe.

Ya ce wannan wani buri ne da al’ummar Gombe da sauran yankin Arewa maso Gabas suka daɗe suna fata, domin aikin zai taimaka wajen samar da kayan gini cikin sauƙi tare da ƙara samar da guraben ayyukan yi.

Kwairanga ya bayyana farin cikinsa da yadda faɗaɗa Ashaka Cement ya zama ɗaya daga cikin manyan tsare-tsaren HBM Nigeria Plc, yana mai cewa yana sa ran halartar bikin ƙaddamar da sabon ɓangaren da za a faɗaɗa nan gaba.

Ya kuma sake taya kamfanin murnar wannan gagarumin sauyi, tare da yi masa fatan samun nasara da ci gaba a sabon babin da ya buɗe a tarihin kamfanin.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: An Karrama Darakta Janar Na DSS Bisa Ƙoƙarinsa Na Inganta Alaƙar Hukumomin Tsaro Da Kafafen Yaɗa Labarai
Next Post: Jihar Gombe Ta Karbi Bakuncin Taron Tsaro Tsakanin DIG Da Masu Ruwa Da Tsaki

Karin Labarai Masu Alaka

Koriya Ta Arewa Ya Goyi Bayan Iran Wajen Zaben Sabon Jagora Mojtaba Khameni Afrika
Amurka Ta Sanya Hanu Kan Yarjejeniyar Kiwon Lafiya Da Ƙasashen Madagascar, Saliyo, Botswana, Ethiopia Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnatin Bauchi: Ta Kaddamar Da Kwamitin Ma’adanai Labarai
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Senegal Yaki Amincewa Da Hukuncin CFA Afrika
Jami’ar Tarayya A Gombe Ta Karyata Harin ‘Yan Bindiga Najeriya
Kasashen Amurka,Israela Da Iran Sun Amince Da Dakatar Da Yaki Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • CAF Ta Ci Tarar Ƙasar Masar Dala 5,000 AFCON 2025 Wasanni
  • Anakan Bincike Wajen Gano Dan Bindigar Da Ya Kashe Dalibai Biyu A Jihar Rhode Island Amurka
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • An Kashe Falatsinawa Biyar A Wani Hari Da Isra’ila Takai Wata Makaranta A Gaza Tsaro
  • Gombe Ta Yi Kira Ga Jami’o’i Su Tallafa Wa Gwamnati Ta Hanyar Bincike Da Ƙirƙire-ƙirƙire Afrika
  • Shugaba Trump Ya Amince Da Tsawaita Cinikayya Tsakanin Amurka Da Kasashen Afirka Afrika
  • Zulum Ya Rushe Majalisar Zartarwa Ta Jihar Borno Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Yaba Da Hikima Da Jagorancin Sarkin Gombe A Shekaru 12 Na Jagoranci Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.