PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe
Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) reshen jihar Gombe ta bayyana damuwa kan wasu matakan da gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta ɗauka a baya-bayan nan, inda ta zargi gwamnatin da karya ƙa’idodin dimokuraɗiyya da kuma tauye haƙƙin wasu ‘yan jihar. A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na jam’iyyar a jihar, Abdulkadir Ahmad…

