Kasar Saudiya Zata Cika Azumi Talatin
Ba a ga jaririn Watan shawwal ba a Yau laraba saboda haka za a yi karamar Sallah 1447 a ranar juma’a a cewar kwamitin kula da duban wata a kasar. (Kafar SN)
Ba a ga jaririn Watan shawwal ba a Yau laraba saboda haka za a yi karamar Sallah 1447 a ranar juma’a a cewar kwamitin kula da duban wata a kasar. (Kafar SN)
Ranar talata, Isra’ila ta bada sanarwar ta kashe babban jami’in tsaro a Iran, jami’in Farisa mafi-girma da ta auna hari akansa tun fara bayanin ranar farko na fara yakin, a yayinda wani jami’in kasar yake cewa, sabon shugaban addinin kasar ya ki amincewa da tayin sassauta rikicin, da wata kasa mai shiga tsakani ta gabatar…
Ci Gaba Da Karatu “Isra’ila Ta Kashe Babban Jami’in Tsaron Iran Ali Larjani” »
A Senegal, masu goyon bayan a kafa dokoki masu tsanani kan ‘yan luwadi da madugo a kasar, sunyi musayar ra’ayi kan yadda za su kaddamar da gangami da neman goyon bayan jama’a da wata kungiya dake Amurka mai goyon bayan iyali irin na gargajiya, wacce take cewa luwadi barazana ce kan kiwon lafiyar jama’a, kamar…
Ci Gaba Da Karatu “Anfara Gangamin Kafa Dokoki Masu Tsanani Ga ‘Yan Luwadi A Senegal” »
Kasashen Canada, da Faransa, da Jamus, da Italiya, jiya Litinin sukayi kira cewa tilas Isra’ila ta kaucewa “matakin tura sojoji cikin Lebanon,” saboda zai haifarda mummunar sakamako kan zamantakewa, kamar yadda suka fada a cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da suka fitar. An jefa Lebnnon cikin yakin na gabas ta tsakiya ne ranar 2…
Ci Gaba Da Karatu “An Gargadi Kasar Canada Game Da Tura Sojoji Lebanon” »
Kasashen da suke yankin Gulf da farko ba su goyi bayan Amurka ta kai hari kan Iran ba, amma yanzu suna kira da Amurka kada ta dakatar da yakin, ta yadda zata kyale gwamnatin da take Tehran da zata ci gaba da barazana ga kadarorin mai da tattalin arzikin da suka dogara akan su, kamar…
Ci Gaba Da Karatu “Kasashen Yankin Gulf Sun Bukaci Amurka Takawo Karshen Iran” »
A ranar Litinin, kasar Kenya ta ce ta cimma yarjejeniya da kasar Rasha cewa ‘yan Kenya baza su kara zuwa dan yiwa Rasha yaki ba, a yakin ta da take yi da Ukraine, bayan da yawan daukan ‘yan Afirka yaki, ya haifar da bacin rai a wasu kasashen na Afirka. Kenya tace an dauki fiye…
Ci Gaba Da Karatu “Kenya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kasar Rasha” »
Da dama daka cikin kasashe ‘yan kawancen Amurka sun yi watsi da kiran da shugaba Donald Trump yayi na su aike da jiragen yaki mashigin ruwa na Hormuz, abinda ya janyo suka daga shugaban na Amurka, wanda ya Zargi kasashen na yamma da nuna rashin godiya bayan shafe shekaru ana mara musu baya. Daga cikin…
Ci Gaba Da Karatu “Kasashen Da Suke Kawance Da Amurka Sun Juyawa Trump Baya” »
Yanzu yaki tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya shiga mako na uku, ba tare da wata alama karara ta tsagaita shi ba, abinda yayi sanadiyyar rufe mashigin ruwa na Hormuz, inda ta nan ne ake jigilar Kashi 20 cikin 100 na man fetur da gas na duniya. Wannan yasa farashin man fetur da sauran makamashi…
Ci Gaba Da Karatu “Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya” »
A Jamhuriyar Congo an kada kuri’a a zaben shugaban kasa ranar Lahadi, wanda ake sa ran zai tsawaita wa’adin mulkin shugaba Denis Sassou Nguesso, daya daga cikin shugabannin Afirka da suka fi dadewa akan karagar mulki, duk kuwa da cewar mutane basu fito da yawaba don kada kuri’unsu. Sassou na fuskantar wani kalubale daga abokan…
Ci Gaba Da Karatu “Ranar Lahadi Anyi Zaben Shugaban Kasa A Congo” »
Kasar Rwanda ta ce zata janye dakarun ta daga yankin Cabo Delgado na kasar Mozambique, inda suke taimakawa wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda, idan kokarin nata baya samun goyon baya na tallafin kudade daga kasashen waje. Dakarun da aka aike su tun shekarar 2021 bayan da Mozambique ta bukaci hakan, sun taimaka wajen kawo kwanciyar…
Ci Gaba Da Karatu “Rwanda Zata Janye Dakaru Daga Mozambique” »