Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Gwamnatin Najeriya Ta Karyata Raɗe-Raɗin Canza Sunan Kasar Da Soke Shari’a A Arewa
Published: May 22, 2026 at 7:46 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Fadar Shugaban Kasar Najeriya ta karyata wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin sauya sunan Najeriya zuwa “United States of Nigeria” tare da soke dokar Shari’a a Arewacin kasar.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar 21 ga watan Mayun 2026, gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin “labarin karya” da wasu ke yadawa domin haddasa rikici da tayar da hankalin jama’a gabanin babban zaben 2027.

Sanarwar ta ce babu wani kudiri da Shugaba Tinubu ke shirin aikewa Majalisar Dokoki ta Kasa mai suna “Project True Federation” kamar yadda ake yadawa.

Fadar shugaban kasar ta zargi masu yada rahoton da kokarin haifar da rabuwar kai da rikicin siyasa a kasar.

“’Yan Najeriya su yi watsi gaba daya da wannan labari saboda masu yada shi makiyan zaman lafiya ne kuma masu neman tayar da tarzoma,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa sauya kundin tsarin mulkin kasa ba abu ne da shugaban kasa ko majalisa za su yi kai tsaye ba, domin akwai matakai masu tsauri da suka hada da samun amincewar kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin kasar da kuma majalisun dokokin jihohi 24.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu na mayar da hankali ne wajen aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin sa ta fara domin inganta rayuwar ’yan Najeriya.

Fadar shugaban kasar ta gargadi jama’a da su rika taka-tsantsan wajen karanta da yada rahotannin karya musamman yayin da harkokin yakin neman zabe ke kara karatowa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Jam’iyyar APC Ta Ayana Jamilu Gwamna A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe
Next Post: APC Ta Bayyana Abba Yusuf A Matsayin Halastaccen Ɗan Takara Bayan Cika Sharudda

Karin Labarai Masu Alaka

Wani Jirgin Kasa Yayi Hatsari A Kudancin Spain Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya Afrika
Ministan Yaɗa Labarai: Ceto Daliban Neja An Samu Natsuwa A Kasa Labarai
Kotu A Abuja Tabawa Goodluck Jonathan Daman Tsayawa Takara Afrika
Fiye Da Fararen Hula 1000 Yunwa Ta Kashe A Sudan Afrika
Farashin Danyen Mai Da Iskar Gas Ya Tashi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki Labarai
  • Shugaba Trump Ya Hana Kaiwa Cuba Man Fetur Daga Venezuela Amurka
  • Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC Afrika
  • Matatar Man Dangote Zata Bada Kwangilar Sayar Da Gas Da Man Jirage Afrika
  • Kotun Kasar Rasha Ta Daure Dan Kasar Belarus Shekarar 22 A Kurkuku Labarai
  • Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai Afrika
  • Tinubu Ya Nada Shugabannin Hukumar NERC Najeriya
  • China Ta Yi Kira Da Kasashen Gabas Ta Tsakiya Su Hada Kai Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.