Kasar Iran ta ce a yau Litinin jakadan ta a kasar Lebanon zai ci gaba da zama a ofishin sa a Beirut, inda tayi watsi da umarnin da ma’aikatar kasashen waje ta Lebanon ta bayar na ya fice daga kasar bata bukatar sa.
Yakin da ake tafkawa tsakanin kungiyar Hezbolla na Lebanon da Isra’ila ya kawo zaman tsami tsakanin gwamnatin Lebanon da Hezbolla da Iran ke marawa baya, inda gwamnatin ke sukar Hezbolla kan shigar da Iran yaki.

A makon da ya gabata ne ma’aikatar harkokin waje ta Lebanon ta bawa Jakadan Iran Mohammed Reza Shibani zuwa 29 ga wannan watan da ya fice daga kasar, saboda ya sabawa tsarin diplomasiyya, ta tofa bakin sa kan harkokin siyasar cikin gida na Lebanon.
Kakakin majalisar Lebanon Nabih Berry, kuma, wanda yake dan Shi’a ne, kuma me goyon bayan Hezbolla, ya kalubalanci shawarar da ma’aikatar harkokin wajen ta yanke, inda yace Shibani yayi zaman sa.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Iran ma Esma’il Baghaei, yace Shibani zai ci gaba da zama a Beirut.


