Tanzania tace ta na sa ran nan da watan Yunin bana, zata rattaba hanu kan yarjejeniyar gina tashar iskar gas da zai ci kudi dala bilyan 42, aikin wadda ya tsaya a baya, wani jami’in kasar ya fada ranar litinin cewa, ana sa ran tashar ta fara aiki ckin shekaru takwas masu zuwa.
Kamfanonin Equinor, da shell sune manya da suke da hanu wajen tafiyar tashar, wadda ake sa ran gano iskar gas da yawansa ya kai galan ko ma’aunin gas fiye da trillion 47. Haka nan kamfanonin Exxon Mobil, da Pavillion, da Medco, tare da kamfanin harkokin mai na kasar Tanzania duka suna da hanun jari a ciki.
An tsaida aikin ne a baya, saboda gwamnati ta kuduri aniyar sauya fasalin kudi a yarjejeniyar da aka kulla.
Tare da irin wannan tashar a kasar Mozambique idan suka fara aiki, za su maida gabashin nahiyar Afirka a zaman babbar tashar samar da makamashin gas ga yankin Asia.
Idan aka kammala aikin gina tashar, jami’an kasar Tanzania suka ce ana sa ran zai samar da ayyukan yi ga mutane sama da dubu dari.


