Ƙungiyar Mata Manoma a Najeriya, wato WOFAN, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Salamatu Garba, ta raba buhunan shinkafa dubu biyar ga mata a jihar Gombe domin tallafa musu wajen inganta rayuwar iyalansu, a wani shiri da aka gudanar domin tunawa da Ranar Mata ta Duniya.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da rabon tallafin, Shugaban WOFAN a Jihar Gombe, Usman Rayyanu Dabai, ya bayyana cewa shirin ya shafi mata a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar da suka haɗa da Gombe, Akko, Yamaltu Deba, Kwami da Dukku.

Ya ce an shirya wannan tallafi ne a wani ɓangare na bikin Ranar Mata ta Duniya, domin ƙarfafa mata da kuma taimaka musu su tallafa wa iyalansu, musamman mazajensu, wajen tafiyar da al’amuran gida.
Rayyanu Dabai ya kuma yi kira ga mata a faɗin Jihar Gombe da su ci gaba da bai wa mazajensu haɗin kai a harkokin gida, domin ƙarfafa zaman lafiya da kyakkyawar rayuwar aure.

A nasu jawaban yayin karɓar tallafin, wasu daga cikin sarakunan gargajiya da suka haɗa da Banban Hakimin Gombe, Alhaji Bappah Ibrahim, Hakimin Bokna, Alhaji Abubakar Usman Deba, da Lamidon Akko, Alhaji Umaru Muhammadu Atiku, sun yaba wa Hajiya Salamatu Garba bisa wannan karamci da ta nuna wa al’ummar Jihar Gombe.
Sarakunan gargajiyar sun kuma buƙaci mata a jihar da su zauna lafiya da mazajensu tare da riƙa ba su goyon baya, domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kan iyalai.

An gudanar da bikin ƙaddamar da rabon tallafin ne a Makarantar Firamare ta Orji Estate da ke Gombe, inda wakilan mata daga kowace ƙaramar hukuma da abin ya shafa suka halarta domin karɓar nasu kaso na tallafin.


