Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika

Kwamitin Ardo Chindo Ya Buƙaci A Hana Mamaye Filayen Kiwo da Gandun Daji
Published: July 28, 2026 at 4:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kwamitin Aiwatar da Fararen Takardar Kula da Filayen Kiwo a Jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Dakta Ardo Chindo Abubakar, ya kai ziyarar aiki zuwa Masarautun Billiri da Pindiga domin ci gaba da wayar da kan al’umma da kuma tabbatar da aiwatar da manufofin gwamnati na samar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.

A lokacin ziyarar a Billiri, Shugabar Ƙaramar Hukumar Billiri, Hajiya Eglah Idris, ta tarbi mambobin kwamitin tare da tabbatar musu da cikakken goyon baya da haɗin kai wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.

Ta roƙi kwamitin da ya yi la’akari da bai wa manoman da suka riga suka noma a cikin filayen kiwo damar girbe amfanin gonakinsu na bana kafin a fara cikakken aiwatar da dokokin, bisa amincewar hakimai da shugabannin ƙauyuka.

Da yake mayar da martani, Shugaban Kwamitin, Dakta Ardo Chindo Abubakar, tare da Daraktan Gandun Daji na Jihar Gombe, Alhaji Musa Suleiman Kumo, sun bayyana cewa wannan shawara abin maraba ne, tare da alƙawarin yin nazari a kanta yayin aiwatar da matakan gwamnati.

Dakta Ardo Chindo ya bayyana cewa kwamitin ya fuskanci ƙalubale a wasu sassan jihar sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma, amma ya jaddada aniyarsa ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

A Masarautar Pindiga kuwa, Hakimin Garin Galadima, Alhaji Muhammad Kawuwa Ahmad, ya ce a wasu lokuta hukumomin gargajiya ba sa samun bayanan wasu matsaloli tun da wuri, lamarin da ke haddasa ta’azzarar rikice-rikice.

Hakimin ya buƙaci al’umma su ci gaba da zaman lafiya da juna tare da mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya domin samun ci gaba.

Shi ma Shugaban Hukumar Raya Karkara ta Pindiga (LCDA), Alhaji Garba Yakubu, Walin Pindiga, ya yaba wa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa samar da yanayi na zaman lafiya da inganta rayuwar al’ummar jihar.

Ya kuma tabbatar wa kwamitin da cikakken goyon baya wajen aiwatar da shawarwarin Farar Takarda domin samar da mafita mai ɗorewa ga rikice-rikicen makiyaya da manoma.

A nasa jawabin, Hakimin Kolmani, Barrista Muhammad Magaji Ibrahim, ya buƙaci a ɗauki tsauraran matakai kan duk masu mamaye filayen kiwo da gandun daji ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce duk wanda aka samu da laifin sayar da filayen kiwo ko hanyoyin shanun gwamnati ya kamata a hukunta shi bisa tanadin doka domin hana sake aukuwar irin wannan matsala.

Har ila yau, Daraktan Gandun Daji, Alhaji Musa Suleiman Kumo, ya yi kira ga masu sare bishiyoyi ba tare da izini ba da su daina wannan danyen aiki, yana mai buƙatar al’ummar jihar su kasance masu bin doka tare da bai wa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya cikakken haɗin kai wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da zaman lafiya a jihar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gidauniyar Jalo Wali Ta Ƙaddamar Da Bada Audugar Mata A Gombe
Next Post: Haɗin Gwiwar GOSERC Da Savannah Zai Ƙarfafa Rarraba Wutar Lantarki A Faɗin Jihar Gombe

Karin Labarai Masu Alaka

Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jami’an Askarawa A Zamfara Sun Kama Na’urorin Fashewa Da Makudan Kuɗaɗe Afrika
Farashin Man Fetur Yakara Tashi Labarai
Nigeria Zata Bude Asusun Dala Bilyan Biyu Don Habaka Sashin Makamashi Labarai
Kungiyoyi Sunyi Hasashen Jinkiri A Bunkasar Tattalin Arzikin Kashen Afirka Afrika
Cutar Kurkunu Ta Kusa Zamowa Tarihi A Duniya Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • UEFA Tana Shirin Janye Barazanar Kauracewa Gasar FIFA
  • Feyenoord Ta Fara Tattaunawa Da Manchester United Kan Daukar Chido Obi Aro 
  • Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Amurka Yace Zasu Kakabawa Mashigar Hormuz Takunkumi Afrika
  • Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar Afrika
  • Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
  • Ambaliyar Ruwa Ya Tilastawa Dubban Jama’a Rasa Muhallensu A Morocco Afrika
  • Gombe Ta Haɗa Kai Da UNICEF Don Kare Yara Daga Tamowa Tun Kafin Haihuwa Afrika
  • An Gudanar Da Jana’izar ’Yan Jaridan Da Suka Rasu A Jihar Gombe Labarai
  • An Yaba Wa Gwamnatin Bauchi Bisa Karban Bakuncin Gasar Polo Wasanni
  • Amurkawa Sun Nuna Bacin Rai Saboda Yawaita Kashe ‘Yan Kasar Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.