JIHAR NASARAWA TA ƊAUKI KYAUTAR KWALLON KAFAR KURAME.
Ƙungiyar Kwallon Kafa na Kurame Deaf, ta jihar Nasarawa a Tarayyar Najeriya ta lashe kofin gasar a bana.
Gasar wadda ta ƙunshi jihohi goma, ciki har da Nasarawa, Rivers, Niger, Kaduna, Kano, Kebbi, da masu masaukin baki, Plateau, Adamawa, Bauchi, da FCT, Abuja, ta fara ne a ranar 19 ga Nuwamba, 2025, a cibiyoyi daban-daban a Jos, Jihar Plateau.
Sakatariyar Wasanni ta Musamman na Jihar Nasarawa, Ms Patricia David Oshuwayine, ita ta wakilci Ma’aikatar Matasa da Ci gaban Wasanni ta Jihar Nasarawa a gasar.
Kwamishinan Ci gaban Matasa da Wasanni na Jihar Nasarawa, Hon. Kwanta Yakubu, ya taya Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Kurame na Jihar murna nasarar da suka samu a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta ƙasa ta karo na 6 da aka gudanar a Jos, Jihar Plateau.
Kwanta ya ce, “Makonni kaɗan da suka gabata, na haɗu da membobin ƙungiyar a sansaninsu da ke Lafia, kafin fara gasar, kuma na ƙarfafa musu gwiwa don su yi duk mai yiwuwa don faranta wa Gwamna Abdullahi Sule da Jihar rai ta hanyar lashe gasar a Jos, kuma zan gabatar da su ga Gwamna.
“A yau, Gwamna Abdullahi Sule da dukkan al’umar Jihar suna alfahari da rawar da ƙungiyar ta taka.
“‘Yan wasanmu masu hazaka sun fafata da manyan ƙungiyoyi daga ko’ina cikin ƙasar, kuma daga ƙarshe sun yi nasara
“Muna yi wa sabbin zakarun ƙasa alƙawarin tarba mai kyau da kuma shirya ya musu liyafa ta musamman a Lafia, Babban Birnin Jiha,” in ji Kwamishinan.
Tawagar ƙungiyar Nasarawa ta samu wannan nasararne bayan da ta doke tawagar ƙungiyar kwallon kafa ta Kurame na Jihar Kaduna da ci 1-0 a ranar Asabar 29 ga watan Nuwamban 2025.
Da yake zantawa da yan jarida mai horas da ƙungiyar na jihar Nasarawa Jafar Umar yace kafin lashe wannan gasar ta wagar Nasarawa ta doke masu ma saukin baki jihar Plateau,Adamawa,Kebbi,da jihar Niger.
Kamar yadda Jami’in hulda da jama’a na Ma’aikatar Matasa da Ci gaban Wasanni na Jihar Nasarawa, Eche Amos ya fitar a wata ta karda da ya rabawa mane ma labarai.



