Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Rikici Ya Barke A Kano Bayan Kashe Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Ladani
Published: December 15, 2025 at 4:18 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Matasa a birnin Kano sun kashe wani matashi da ake zargi da kisan ladanin wani masallaci a Unguwar Hotoro dake birnin Kano, arewa maso yammacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a unguwar Hotoro, inda bayanai suka tabbatar da cewa matashin ya yi wa ladanin, mai suna Zubairu Kasim, yankar rago ne da asubahin ranar Litinin sa’ilin da yake shirin kiran sallar asubahi.

Lokacin da manema labarai suka isa inda abin ya faru, sun iske ƴan’uwa da sauran al’ummar unguwar na zaman makoki bayan jana’izar ladanin.

A lokacin da ya tattauna da ‘yan jarida, ɗan mamacin, Isa Kasim, ya ce: “Da asuba ne mahaifina ya fita kiran sallah, inda ya yi kira na farko sai ya zauna yana ɗan lazimi kafin ya yi kira na biyu kawai, Sai wani ya shiga cikin masallacin da makami, ya kama mahaifina ya danne shi ya masa yankan rago, a taƙaice dai ya cire masa maƙogaro.”

Bayan faruwar haka ne wasu daga cikin matasan unguwar suka taru suka hallaka matashin da ya kashe ladanin.

Isa Kasim ya ƙara da cewa: “Allah ya yi shi ma wanda ya kai harin ba zai tsira ba, ƴan unguwa suka taru har suka cimma wanda ya kashe shi, inda suka kashe shi, shi ma.”

Ya ƙara da cewa “Bayan da ƴan unguwa suka kashe wanda ya kai harin, sai su ka ga maƙogwaron mahaifina a cikin aljihunsa a leda.”

Hukumomi sun tura jami’an tsaro unguwar domin tabbatar da doka da oda bayan ɗan yamutsin da aka samu.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Hukumar NAPTIP Ta Kubutar Da Yara 11 Daga Hannun Masu Safara Mutane
Next Post: AFCON 2025, Jerin Abubuwan Da Aka Haramta Wa Magoya Baya

Karin Labarai Masu Alaka

An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi Labarai
Majalisa Ta Sanya Baki Akan Rikici Tsakanin Dangote Da Hukumar Albarkatun Mai Najeriya
Shugabannin Sojojin Najeriya sun Kai Ziyarar Aiki Maiduguri  Afrika
Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnatin Jihar Kano Zata Kashe Makudan Kudade Ga Jama’ar Kano! Najeriya
Rashin Kyawun Hanyoyi Babbar Matsalace A Najeriya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Limamin Da Ya Ceci Kiristoci Lokacin Rikicin Addini A Jihar Filato Ya Rasu Labarai
  • Ingila, Hauhawar Farashi Yayi ƙasa Sosai Labarai
  • Gwamnan Gombe Ya kori Wasu Hadimansa Bisa Cin Zarafin Kansila Najeriya
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Talata 11.18.2025 Rediyo
  • Gwamnatin Gombe Ta Raba Naira Miliyan 14 Ga Iyalen ‘Yan Jaridan Da Suka Rasu Najeriya
  • Amurka Zata Bada Gudumawar Kudi Dala Bilyan 10 Ga Ayyukan Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiyan Amurka
  • Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Harin Jos Afrika
  • Abu Mafi Daukar Hankali A Wasan Dambe Na Yau Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.