farashin man fetur ya tashi zuwa Kashi 35 cikin 100 a wannan makon bayan da Isra’ila ta kai hari kan mafi girman cibiyar gas ta Iran, yayin da ita kuma Iran din ta mai da martani wajen kai hari kan cibiyoyin makamashin makwabtan ta. Tarayyar Turai tayi kira ga ‘yan kungiyar ta da su cike ma’ajiyoyin da ake tanada gas a hankali domin ya isa yadda ake bukata.
India, wadda ke fama da karancin gas na girki na daya daga cikin kasashen da ta roki Iran ta bari jiragen ta su wuce ta mashigin ruwa na Hormuz. Prime ministan India Nerandra Modi ya gana da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a ranar Asabar.
Kasar Japan ma ta samu lamuni, inda ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi yace fadar gwamnatin Tehran a shirye take ta bar jiragen Japan su wuce ta mashigin ruwa na Hormuz, wanda ke daukan kusan kashi 90 cikin dari na man da ake shigowa da shi Japan.


