Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Sakataren Tsaron Amurka Yace Yaki Tsakanin Amurka Da Iran Zai Dauki Sabon Salon
Published: March 31, 2026 at 8:47 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya fada ranar talata cewa, kwanaki masu zuwa za su kasance masu gauni a yakin da Amurka take yi da Iran, ya kuma gargadi Tehran cewa, yakin zai kazance idan bata yarda aka cimma yarjejeniya ba kawo karshen yakin ko tsagaita wuta ba.

Rundunar juyin juya hali ta Iran, ta maida martani inda tayi barazanar auna hare haren kan kamfanonin Amurka da suke yankin daga ranar Laraba, rundunar tace kamfanoni da zata auna sun hada da Microsoft, da Google, da Apple, da Intel, da IBM, da Tesla, da kuma Boeing.

Tunda farko, Iran ta cinna wuta kan wani jirgin ruwa shake da mai, ba nesa da gabar Dubai, harin da Farisar ta kai na baya bayan nan kan jiragen kasuwanci a yankin na Gulf ko a mashigin ruwan Hormuz, tun bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare hare kan kasar ranar 28 ga watan Febwairu.

Jiya Litinin, shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar zai yi kaca-kaca da da cibiyoyin samarda makamashi na Iran, idan bata amince da yarjejenyar zaman lafiya, kuma ta bude mashigin ruwa na Hormuz ba, hanya ta cikin ruwa mai tasiri ga jigilar makamashi da duniya take amfani da shi wadda Iran ta rufe shi.

A yau talatan shugaba Trump ya soki kasashe da basu taimaka a yakin ba, da suka hada da Faransa da kuma Ingila, yace su gwada bajinta ko kawarin guiwa da suka rasa a baya, su kwato mashigin ruwa na Hormuz, su samowa kan su mai. Faransa da Italiya sun nuna rashin amincewar su da wasu matakan sojin da Amurka da Isra’ila suka dauka, kamar yadda wasu majiyoyi suka fada,wadda yake nuna rarrabuwar kawuna tsakanin kasashe dake cikin kungiyar tsaro ta NATO.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Kashe-kashen Jos Da Kaduna
Next Post: Farashin Mai Yana Cigaba Da Karuwa

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Kasar Venuzuela Zasu Fara Komawa Gida Amurka
Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
Rikicin Gabas Ta Tsakiya Ya Haifar Da Tsadar Man Fetur A Najeriya Afrika
Rasha Takai Sabbin Hare-Hare Akan Wasu Biranen Ukraine Tsaro
Haryanzu Abubakar Malami Da Dansa Suna Hannun Hukumar EFCC Labarai
Gwamnatin Amurka Na Kokarin Watsi Da Tsohuwar Dokar Jones Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya Siyasa
  • Sanyin Hunturu Yayi Ajalin ‘Yan Cirani A Morocco Afrika
  • Kasar Ukraine Tayi Watsi Da Shiga Kungiyar NATO Labarai
  • An Gano Kwale-Kwalen Fir’auna A Birnin Masar Afrika
  • Fiye Da Mutane Miliyan Hudu Suna Fuskantar Barazanar Yunwa A Somaliya Sauran Duniya
  • Dangote Ya Rage Farashin Mai A Najeriya Labarai
  • Sojoji Sun Murkushe ‘Yan Bindiga A Jihar Sakkwato Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.