Da yai magana kan rikicin na gabas ta tsakiya, shugaban majalisar tarayyar turai, Antonio Costa, ya fada ranar talata cewa Rasha ce take cin ribar yakin da ake yi a gabas ta tsakiya, ganin farashin mai ya tashi, kuma ya kauda hankali daga yakin da take da Ukraine.
“Zuwa yanzu dai kasa daya ce ta sami nasarar wannan yaki,” itace Rasha, Costa ya fada a wani jawabi da yayi wa jakadun Kungiyar tarayyar turai.
Antonio Costa, ya jaddada bukatar kungiyar tarayyar turai ta kare tsarin duniya na bin doka da oda, wadda yace ahalin yanzu Amurka take yi wa kalubale, daga nan ya shawarwaci duka sassa a rikicin na gabas ta tsakiyya, su koma teburin shawarwari.
Ahalinda ake ciki kuma, farashin mai ya fadi da kamar kashi 15 cikin dari ranar talata, kwana daya bayanda mai yayi tashin goron zabbi, rabon da ya kai haka tun 2022, faduwar farashin ya biyo bayan kalaman shugaban Amurka Trump cewa yakin ya kusa zuwa karshe.
Yau mai da ake kira Brent ana cinikinsa kan dala 84 da centi 73 kan ko wani gangar danyen mai, yayinda wadda ake kira West Texas shi kuma ya tashi kan dala 80 da centi 31. Farashin ya kara faduwa, bayan da ministan makamashi na Amurka Chris Wright ya rubuta a shafinsa na X cewa, sojojin Amurka sun taimaka an wuce da mai ta mashigan ruwa na Hormuz.
Wannan lamari na tsadar mai yana kalubale ga rinjayen da jam’iyyar Republican take dashi a zaben rabin wa’adi mai zuwa, kamar dai yadda masu nazarin harkokin yau da kullum suke hasashe.
Har yanzu dai kan yakin na gabas ta tsakiya, Australia zata tura jirgin leken asiri zuwa gabas ta tsakiya, kuma zata aike da makamai masu linzami zuwa hadaddiyar daular larabawa, amma ba zata tura sojojinta na kasa zuwa Iran ba, PM kasar Anthony Albanese ya fada a ranar talata.
Albanese yace, taimakon da Australia take da kayan yaki, zai taimakawa kasashe da suke yankin Gulf su kare kan su daga hare hare daga Iran ba babu hujja.


