Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Sojojin Faransa Sun Karyata Zargin Bobi Wine
Published: January 26, 2026 at 9:13 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban rundunar sojojin Uganda Muhoozi Kainarugaba ya musanta zargin da dan jam’iyyar adawa Bobi Wine ya yi, na cewa sojoji sun kai wa matar sa hari lokacin da suka je samame gidan sa cikin dare.

Wine, wanda sunan sa na gaske shi ne Robert Kyagulanyi, ya yi ikirarin cewa sojoji sun shiga gidan sa da tsakar dare, a unguwar Magere da ke wajen garin Kampala, suka ci zarafin ma’aikatan sa, kuma suka shake matar sa, Barbara Kyagulanyi, abinda ya kai har sai da ta je asibiti neman magani.

Wine, da ya shiga buya tun bayan gudanar da zaben da ya ke kalubalanta, yace baya gida a lokacin da abin ya faru.

Kainarugaba, wanda da ne ga shugaban kasar uganda, Yoweri Museveni, ya yi watsi da wannan zargi, a wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, inda ya ce sojoji basa dukan mata. Ya kara da cewa, bamu da lokacin su, muna neman matsoracin mijin ta ne ba ita ba.

Bobi Wine, wanda da mawaki ne ya koma dan siyasa, ya zargi dakarun tsaron Uganda da cin zarafi tun bayan gudanar da zaben shugaban kasa ranar 15 ga Watan Janairu, wanda Yoweri Museveni ya yi nasarar lashewa da kashi 71.6 cikin 100 na kuri’un da aka jefa. Wine, wanda ya zo na biyu ya ki yarda da sakamakon zaben da yake ganin an tafka magudi.

Ba’a samu sahihin dalilin da ya sa sojoji ke neman Wine ba.

Labarai, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Kungiyar ‘Yan Ta’adda Masu Alaka Da ISIS Sun Kashe Mutane A Congo
Next Post: Sanyi Mai Tsanani Da Dusar Kankara Ya Tsaida Al’amura A Amurka

Karin Labarai Masu Alaka

Magajin Garin Istanbul Dake Kurkuku Ya Bukaci A Gudanar Da Zabe Labarai
An Kaiwa Sojojin Ghana Hari A Lebanon Afrika
Farashin Mai Ya Ragu A Kasuwar Duniya Amurka
Shugaba Trump Yace Zai Dakatar Da Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika
Shugaban Hukumar NAHCON Ya Ajeye Mukaminsa Labarai
Wani Dan Bindiga Ya Harbi Dakarun Tsaron Cikin Gida Su Biyu A Washington DC Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Tana Saka Ido Akan Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Shugaban Ƙasar China Zai Karbi Bakwancin Shugaban Koriya Ta Kudu Afrika
  • Wasu Yara 50 Sun Kubuta Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai
  • Kotu A Kasar Tunisiya Ta Daure Wani Babban Dan Kasuwa Da Wasu ‘Yan Majalisa Afrika
  • Amurka Zatayi Amfani Da Sansanonin Birtaniya Amurka
  • Babban Bankin Najeriya Ya Rage Kudin Ruwa Da Kashi Daya Cikin Dari Labarai
  • Kamfanin NNPC Yana Tattaunawa Da Wani Kamfanin Kasar China Labarai
  • An Kai Shugaban Kasar Venezuela Kotu Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.