Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika

Tarayyar Turai Zasu Kirkiro Sojojin Haɗin Gwiwa
Published: January 22, 2026 at 7:45 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 22, 2026

A halin da ake ciki, Kasar Spain ta yi kira ga Tarayyar Turai da ta dauki matakan kirkiro rundunar sojojin hadin guiwa ta Kasashen Tarayyar Turai, domin ta zamo hannunka mai sanda ga duk wani mai neman nuna musu yatsa.

Ministan harkokin wajen Spain, Jose Manuel Albares ya fada ranar laraba cewa ya kamata kasashen Turai su fara da hada hancin kayan tsaron da suke da su da hade masana’antunsu na tsaro, kafin su kafa runduna guda.

Albares yace a zahiri ne cewa akwai damuwa a kan ko al’ummar kasashen Turai zasu yarda da kafa runduna guda, amma kuma yace samun runduna guda ta fi tasiri a kan rundunoni har 27 dabam-dabam.

Wannan kira nasa yana zuwa kafin wani taron gaggawa da shugabannin Tarayyar Turai zasu yi ranar alhamis a Brussels domin maida martani bai daya ga barazanar shugaban Amurka Donald Trump na saye ko kwace yankin Greenland.

Wani kakakin majalisar TT ya tabbatar da cewa za a gudanar da wannan taron gaggawa na ranar alhamis duk da cewa shugaba Trump ya fada cewa shi da sakatare janar na NATO, Mark Rutte sun cimma daidaituwa kan yadda za a takali batun na Greenland.

Albares yace ba manufar wannan runduna da yake kiran da a kafa ce ta maye grbin NATO ba, amma kuma akwai bukatar nunawa duniya cewa ba wani wanda zai iya yi ma Turai barazanar soja ko ta tattalin arziki.

Wannan ra’ayi na kafa rundunar sojojin hadin guiwa ta kasashen Turai ba sabon abu ba ne. An fara gabatar da shi tun shekarar 1951 domin tunkarar tsohuwar Tarayyar Soviet da tabbatar da cewa ko kasar Jamus ta sake yin damara ba zata yi barazana ga makwabtanta ba. Majalisar dokokin kasar Faransa ita ce ta kashe wannan yunkurin ta hanyar jefa kuri’ar kin yarda da shi.

Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kungiyar Maharba Da ‘Yan Sintiri Sun Samu Kyautar Motoci
Next Post: Boko Haram Sun Farmaki Sansanin Sojoji A Borno

Karin Labarai Masu Alaka

Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Jakadan Israela Ya Fice Daga Kasar Afrika
Majalisar Kwararrun Iran Ta Sanar Da Sabon Shugaban Addini Afrika
‘Yan Bindiga Sun Jikkata Mutane A Arewacin Kasar Benin Afrika
Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
Farashin Gangar Mai Yayi Gagarumar Fadi A Kasashen Duniya Labarai
Gwamnatin Bauchi: Ta Kaddamar Da Kwamitin Ma’adanai Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi
  • Ceferin Ya Ce Ba Zai Yi Takarar Shugabancin FIFA Ba
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Alkalan Wasannin Kwallon Kafa A Ghana Zasu Samu Inshora Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika
  • An Bukaci Mabiya Addinin Kirista Da Suyi Koyi Da Rayuwar Yesu Najeriya
  • ‘Yan Sandan Habasha Sun Kama Dubban Albarusai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
  • An Zargi Kasar Eritrea Da Cin Zarafin Sojojin Habasha Afrika
  • Dan Wasan Baya Na Chelsea, Disasi, Zai Yi Gwajin Lafiyarsa A Crystal Palace Wasanni
  • Zamfara: Sai Mun Hada Kai Don Kawo Karshen Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.