Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a matsayin magajin Malam Aminu Kano wajen kishin al’umma da jajircewa kan walwalar jihar Kano.
Tinubu ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon taya murna da ya aike wa gwamnan bisa cika shekaru 63 da haihuwa.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar Shugaba Tinubu, sauƙin kai, tawali’u da kuma jajircewar Gwamna Abba Kabir Yusuf sun bayyana karara a yadda yake tafiyar da al’amuran mulki a jihar Kano.
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa yana da cikakken tabbaci cewa Gwamna Yusuf yana bin sahun hangen nesa da tafarkin Malam Aminu Kano wajen jagorancin jihar, wadda ke da muhimmiyar rawa a siyasar Arewacin Najeriya.
Tinubu ya ce jajircewar gwamnan wajen kare haƙƙin talakawan birni da na karkara na daga cikin manyan dalilan da ke tabbatar da hakan.
A cewarsa, shirye-shiryen sabunta birane da gwamnatin Kano ta ɓullo da su, musamman gina gadoji da tituna masu tsawon kilomita biyar biyar a kowace ƙaramar hukuma, sun nuna ƙwazon shugabancin gwamnan.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya yaba da ayyana dokar ta baci da Gwamna Yusuf ya yi a ɓangaren ilimi, inda ya ce hakan ya haifar da gagarumar ci gaba, musamman yadda ɗaliban jihar Kano suka samu sakamako mai kyau a jarabawar NECO.
A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf fatan tsawon rai da ƙarin shekaru na shugabanci masu albarka, tare da fatan ganin ƙarin ci gaba da bunƙasuwar jihar Kano.


