Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Ziyarci IBB
Published: January 20, 2026 at 4:57 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ziyarci tsohon shugaba na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, a gidansa dake Minna ranar Litinin, yayin da ake ta rade-radin alakarsu da shirye-shiryen siyasa kafin zaben shugaban kasa na 2027.

Rahotanni sun nuna cewa tsofaffin shugabannin biyu sun yi ganawar sirri na tsawon mintuna 30 kafin Obasanjo ya koma filin jirgin sama.

Ganawar ta janyo hasashe a cikin ‘yan siyasa cewa tana da alaka da shirye-shiryen samar da tikitin hadin gwiwa ta Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso a karkashin ADC, domin kalubalantar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Har yanzu Obasanjo da Babangida ba su yi wani bayani kan rade-radin ba, amma ganawar ta Litinin na kara karfafa hasashen ci gaba da shirin siyasa na hadin gwiwar ‘yan takara.

Siyasa

Post navigation

Previous Post: Hukumar NAHCON Ta Kamallah Shirye Shiryen Hajjin 2026 A Kasar Saudiya
Next Post: Togo Ta Kama Tsohon Shugaban Kasar Burkina Faso Saboda Kitsa Juyin Mulki

Karin Labarai Masu Alaka

Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe Afrika
Gwamnatin Gombe: Babu Hannun mu a Cin Zarafin Kansilan Mazabar Shamaki Siyasa
Gurbin Yaya Tongo: INEC Ta Tsayar Da 19 Ga Satumba Don Zaɓen Cike Gurbi Afrika
PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe Afrika
Hukumar Zaben Najeriya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa Labarai
Sojojin Faransa Sun Karyata Zargin Bobi Wine Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tsananin Sanyi Ya Kashe Mutane 38 A Amurka Amurka
  • Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Da Ya Rutsa Da Antothy Joshua Najeriya
  • An Kashe Mayakan Sakai 67 A Pakistan Sauran Duniya
  • Kotu A Najeriya Ta Kame Mutane Bisa Zargin Ta’addaci Afrika
  • NAHCON Ta Yaba da Nasarar Hajjin 2026, Ta Fara Shirin Hajjin Shekara Mai Zuwa Amurka
  • Kasar Jamus Ta Haramtawa Yara Kasa Da Shekaru 14 Hawa Dandalin Sada Zumunta Labarai
  • Kadan Daga Cikin Abubuwan Da Suka Faru A 2025 A Nan Amurka Amurka
  • Nuhu Ribadu Ya Mika Dalibai 100 da Aka Ceto Ga Gwamnatin Jihar Neja Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.