Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnan Jihar Kano Ya Fice Daga Jam’iyar NNPP
Published: January 23, 2026 at 4:16 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), yana mai danganta matakin da tsanantar rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar da kuma buƙatar kare muradun al’ummar jihar Kano gaba ɗaya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a.

A cikin wasiƙar da ya aike wa Shugaban mazabar Diso-Chiranchi na jam’iyyar NNPP a Ƙaramar Hukumar Gwale, gwamnan ya sanar da janyewarsa daga jam’iyyar, wanda zai fara aiki daga ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.

“Ina rubuta wannan wasiƙa cikin matuƙar godiya domin sanar da shugabannin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) cewa na yanke shawarar ajiye kasancewata ɗan jam’iyyar, daga ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.”

Gwamna Yusuf ya bayyana godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da kuma goyon bayan da ya samu tun farkon tafiyarsa ta siyasa a ƙarƙashin NNPP.

Ya kuma yi nuni da cewa jam’iyyar na fuskantar rikice-rikice na cikin gida da kuma ƙalubalen shari’a da suka daɗe suna dagula tsarinta a matakin ƙasa.

A cewarsa, rikice-rikicen sun haifar da rarrabuwar kawuna tare da raunana haɗin kan jam’iyyar.

Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan zurfin nazari, kuma bisa la’akari da muradun jama’a kawai.

Ya jaddada cewa ya ɗauki wannan mataki ne cikin kyakkyawar niyya ba tare da wata ƙiyayya ba.

“Na ɗauki wannan mataki cikin kyakkyawar niyya, ba tare da wata muguwar manufa ko ƙiyayya ba, tare da ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar Kano.”

Gwamnan ya fice tare da mambobi 21 na Majalisar Dokokin jihar Kano, mambobi 8 na Majalisar Wakilai ta Tarayya, da kuma shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Sakataren jam’iyyar NNPP na Ward ɗin Diso-Chiranchi, Kabiru Zubairu, ya tabbatar da karɓar wasiƙar tare da yabawa gwamnan bisa ayyukan ci gaba da ya aiwatar a fannoni daban-daban.

Siyasa

Post navigation

Previous Post: Tsohon Lauyan Amurka Jack Smith Ya Fadi Maganganu Game Da Donald Trump
Next Post: Kasar Uganda Ta Tsare ‘Yan Jam’iyyun Adawa Dubu Biyu

Karin Labarai Masu Alaka

Sanata Goje: Sakamakon Zaben Daga Abuja Zai Fito Afrika
Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika
China Ta Kori Wakilan Majalisar Dokoki Uku A Kasar Labarai
Jam’iyar NNPP: Abba Kabir Yusuf Yaci Amanar Mu Siyasa
Gwamna Abba Ya Gana Da Kwankwaso Kamun Ganawarsa Da Tinubu Siyasa
Jagoran Kwankwasiya A Najeriya Ya Koma Jam’iyar ADC Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Matsalolin Masarautun Kano Sun Kawo Karshe Najeriya
  • Wata Kotu A Abuja Ta Wanke Abba Kyari Afrika
  • Mutum Mafi Tsufa A Saudiyya Ya Rasu Yana Da Shekaru 142 Labarai
  • Ana Zargin Tsohon Shugaban Kasar Philippines Da Ta’addaci A Lokacin Mulkinsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau Ya Koma Jam’iyyar APC Afrika
  • Dogarawan Ruwa Na Amurka Suna Yunkurin Shiga Wani jirgin Dakon Mai Da Aka Allakan Ta Da Venezuela Labarai
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa
  • Hukumar MDD Tace Wadanda Suka Mutu A Harin Sudan Sun Haura 70 Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.