Zai yi wuya a wuni mutum bai ji an ba da labarin wani tsoho kai ko matashi mai tashe ya yi wa wata ‘yar yarinya da wata ma ba a gama goyon ta ba fyade, ko kuma yara maza ma ba su tsira daga labarin yin luwadi da su ba daga mutanen da ke kusa da su ko kula da su a matsayin masu kai su makaranta ko koya mu su karatu sai a buge da muguwar dabi’ar.
Najeriya na da akasari mafi yawan jama’ar ta matasa ne kuma yawancin jama’ar na da addini da al’adu amma duk da haka a kan samu karuwar bata gari da sauran miyagun iri; da hakan ba ya rasa nasaba da rashin hukuncin da ya dace da masu laifin.
Mairo Mudi ta kungiyar “media for morals” na daga mata da ke kamfen din kiran samun dokoki masu tsauri don yaki da fyade.

Ta bukaci masu tsara dokoki su bullo da hukunci mai tsanani ga duk wanda a ka samu da laifin da hakan kar ya gaza daurin rai da rai koma kawar da miyagun irin daga doron kasa.
A Abuja majalisar tallafawa shugaban kasa wajen tsara manufofi PSC ta ce lauyoyin ta na shirya kudurin doka mai tsanani kan wannan kalubalen.
Gidado Ibrahim shi ne daraktan labaru na majalisar.
Da alamu fitowar da matar mawakin nan Busola Timi Dakolo ta yi da zargin mai bushara na majami’ar COMMONWEALTH OF ZION Pastor Biodum Fatoyinbo da yi ma ta fyade tun ta na karama, ta karfafawa mata da dama guiwa wajen baiyana irin wannan cin zarafi da a ka taba yi mu su.


