Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kotu Tayi Watsi Da Tarukan ADC Bangaren David Mark
Published: April 29, 2026 at 2:12 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: April 29, 2026

Kotun Tarayya ta hana INEC amincewa da tarukan jam’iyyar ADC da kwamitin Mark ya shirya

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a Najeriya ta umarci Hukumar Zabe ta  (INEC) a kasar da kada ta amince ko ta shiga cikin duk wani taron zaɓen shugabannin jihohi (state congresses) da kwamitocin da shugabancin rikon ƙwarya na African Democratic Congress (ADC) suka shirya.

Da take yanke hukunci a ranar Laraba, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa alhakin gudanar da irin waɗannan taruka na jihohi yana hannun kwamitocin zartarwa na jihohi na jam’iyyar, ba shugabancin ƙasa ba.

Kotun ta kuma tabbatar da cewa wa’adin shekaru huɗu na kwamitocin aiki na jihohi da kwamitocin zartarwa na jihohi na jam’iyyar ADC na nan daram, kuma suna ci gaba da aiki har sai an gudanar da sahihan taruka bisa ƙa’ida tare da kiran babban taron ƙasa.

Haka kuma, Mai Shari’a Abdulmalik ta ce babu wani tanadi a cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ko na jam’iyyar da ke bai wa kwamitin rikon ƙwarya na ƙasa, ƙarƙashin jagorancin David Mark, ikon naɗa kwamitocin da za su gudanar da tarukan jihohi.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/581/2026 da wasu masu ƙara suka shigar, suna ƙara a madadinsu da kuma a madadin dukkan shugabannin jihohi da kwamitocin zartarwa na jihohi na jam’iyyar ADC.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe
Next Post: Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano

Karin Labarai Masu Alaka

Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Ummulkhairi Afrika
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki Labarai
Lakurawa Sun Kashe A Ƙalla A Mutane 34 A Jihar Kebbi Labarai
Harin Jirgi Maras Matuki Ya Hallaka Mutane A Sudan Labarai
Jami’an Shiga Da Fice A Afirka Ta Kudu Sun Tafka Badakalar Kudade Afrika
Tinubu: Mun Ware Biliyan 42 Don Inganta Lafiyar ‘Yan-Kasa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tsohon Dan-Takarar Gwamnan PDP A Gombe Ya Shiga ADC Siyasa
  • Hukumar Raya Birane Ta Rushe Gine-Ginen Da Suka Keta Dokokin Tsara Birane A Gombe Labarai
  • Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe Afrika
  • Sojojin Amurka Sun Kashe Wasu Fararen Hula Ba Dalili Amurka
  • Gwamnonin Arewa Maso Yammacin Najeriya Sun Halarci Taron Inganta Makashi A Birnin Landan Afrika
  • Meyasa Israela Take Hana Kaiwa Gaza Kayan Tallafi Afrika
  • Rundunar Sojin Najeriya Ta Kubutar Da Wasu Mutane 31 Da Aka Yi Garkuwa Dasu Afrika
  • FIFA, Ta Tabbatar Da Ranar Mika Sunayen ‘Yan Wasa AFCON 2025. Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.