Gwamnatin Najeriya Ta Jaddada Aniyarta Ta Daƙile Yaɗuwar Makamai Ba Bisa Ƙa’ida Ba
A ci gaba da aiwatar da ƙudirin Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na dawo da cikakken tsaro a faɗin Najeriya, Hukumar Kula da Ƙananan Makamai da Makamai Masu Sauƙin Sarrafawa ta Ƙasa (NCCSALW), ƙarƙashin Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), ta lalata makamai 2,809 da jami’an tsaro suka kwato daga hannun…

