Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Amurka Tayi Barazanar Zata Rage Tallafin Da Take BayarwaSudan Ta Kudu, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Farashin Mai Ya Fadi Fiye Da Dala Daya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC
Published: December 9, 2025 at 5:19 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: December 9, 2025

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya sanar da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya,

Gwamna Fubara dai ya sanar da sauya sheƙar ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati da ke birnin fatakwal na jihar Rivers.

Wannan dai na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da ƴan majalisar jihar 15 tare da kakakin majalisar suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ta APC.

Masu fashin baƙi dai na ganin sauya sheƙar ta Fubara ba lallai ta yi wa ministan Abuja, Nyesom Wike daɗi ba kasancewar shi ne babban abokin hamayyarsa, inda rikici ya kai har shugaba Tinubu ya saka wa jihar dokar ta-ɓaci ta watanni shida da ta tilasta Fubara sauka da kujerar gwamnan na tsawon watannin.

A watan Satumbar da ya gabata ne Fubara ya koma bakin aikinsa bayan ƙarewar wa’adin watannin shida na dokar ta ta-ɓacin da ta fara aiki a watan Maris a jihar sa.

Bisa tsarin siyasa, gwamnan jiha shi ne jagoran jam’iyya inda yanzu haka Fubara zai kasance jagoran jam’iyyar APC a jihar Rivers.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Ga Alamu Jakuna Za Su Bace A Doron Kasa Nan Da Shekaru 5
Next Post: Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Tayi Barazanar Zata Rage Tallafin Da Take BayarwaSudan Ta Kudu, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kirana Ga ‘Yan Siyasar Arewa, Su Jira Sai 2031- Akume Labarai
An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Guinea Bissau Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ministan Tsaron Najeriya Badaru Yayi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike a Tituna
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000
  • Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakuncin Wasannin Afirka Na 2031.
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Rediyo
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Shin Ko Ganawar Zelensky Da Macron Zata Haifar Da ‘Da Mai Ido? Labarai
  • Isra’ila Ta Dau Alwashin Kawo Karshen Falasdi Labarai
  • Wasu Zakaru Da Suka Samu Karramawar Hukumar CAF Ta Afrika Wasanni
  • ‘Yan Wasan Kwallon Kafar Najeriya A Shirye Suke Wasanni
  • Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa
  • Kotun Tarayya Ta Yankewa Nnamdi Kanu Daurin Rai-da-Rai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Chelsea Tayi Kaca-Kaca Da Barcelona A Gasar UCL Wasanni
  • Ga Dukkan Alamu Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Bai Kare Ba Sauran Duniya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.