Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15 Afrika
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe Afrika
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya Afrika
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu Kiwon Lafiya
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin Afrika

NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa
Published: August 7, 2026 at 6:40 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Majalisar Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen jihar Gombe, ta amince da kafa Kwamitin Da’a da Ladabtarwa da kuma Kwamitin Jagoranci kan Hulɗa da ‘Yan Takarar Jam’iyyun Siyasa gabanin Babban Zaɓen shekarar 2027.

An cimma wannan matsaya ne a taron Majalisar Ƙungiyar (Congress) da aka gudanar a zauren taro na Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Tsare-tsare da Al’adu ta Jihar Gombe, inda mambobi daga rassa daban-daban suka tattauna kan harkokin ƙungiyar da kuma makomar aikin jarida.

Kwamitin Da’a da Ladabtarwar, mai mambobi biyar, wanda Mista Peter Mele ke jagoranta, an kafa shi ne domin tabbatar da bin ƙa’idojin aikin jarida, kiyaye ɗa’a da ladabtar da duk wani memba da ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙungiyar.

Hakazalika, Majalisar ta kafa Kwamitin Jagoranci mai mambobi goma, ƙarƙashin shugabancin Chika Udenkwo, domin tsara tattaunawa tsakanin kafafen yaɗa labarai da ‘yan takarar jam’iyyun siyasa kafin zaɓen 2027.

An ce kwamitin zai shirya zaman tattaunawa da zai bai wa ‘yan takara damar gabatar da manufofinsu da tsare-tsaren ci gaba ga al’umma ta hanyar kafafen yaɗa labarai, domin bai wa masu zaɓe damar yanke hukunci bisa sahihan bayanai.

Majalisar ta kuma yi kira ga ‘yan siyasa, magoya bayansu da sauran masu ruwa da tsaki da su guji kalaman ƙiyayya, yaɗa labaran ƙarya, tunzura jama’a da duk wani nau’in tashin hankali da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin Jihar Gombe.

Ta buƙaci jam’iyyun siyasa su mayar da hankali kan bayyana manufofinsu da shirye-shiryensu maimakon siyasar cin mutunci, yayin da shirye-shiryen Babban Zaɓen 2027 ke ƙara ƙamari.

Majalisar ta yabawa Gwamnatin Jihar Gombe bisa ayyukan ci gaba da take aiwatarwa, tabbatar da zaman lafiya da kuma goyon bayan da take bai wa aikin jarida.

Haka kuma, ta roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta kammala ginin Sakatariyar NUJ tare da miƙa shi ga ƙungiyar, tana mai cewa hakan zai ƙara inganta gudanar da ayyukanta.

Majalisar ta kuma buƙaci gwamnatin jihar ta taimaka wajen samar da sabuwar motar ƙungiyar domin maye gurbin wadda ta lalace a hatsarin mota da ya yi sanadin rasuwar wasu mambobinta.

Bugu da ƙari, Majalisar ta amince da kafa wani kwamiti da zai shirya Taron Zaman Lafiya, wanda zai haɗa jam’iyyun siyasa da ‘yan takara domin ƙarfafa siyasa cikin lumana, fahimtar juna da kuma tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya a Jihar Gombe.

Da yake jawabi, Shugaban NUJ na Jihar Gombe, Kwamared Faruk Mu’azu, ya yabawa Kwamishinan Yaɗa Labarai, Tsare-tsare da Al’adu bisa samar da kyakkyawan wurin gudanar da taron da kuma ci gaba da tallafa wa walwala da bunƙasa aikin ‘yan jarida a jihar.

Majalisar ta kuma gode wa dukkan mambobinta bisa halartar taron, gudummawar da suka bayar da kuma jajircewarsu wajen bunƙasa haɗin kai da ci gaban ƙungiyar.

Sanarwar ta fito ne ɗauke da sa hannun Sakatare, Shuaibu Umar, a madadin Kwamitin Shirya Sanarwar Taron.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Hukumar UBRBDA Ta Fara Raba Kayan Noma A Gombe, Yobe Da Borno
Next Post: Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Ce Albashin ₦70,000 Ya Gaza Biyan Bukatun Ma’aikata

Karin Labarai Masu Alaka

An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya Afrika
Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai
Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi Afrika
Ganduje Ne Yasa Aka Kama Ni Inji Muhuyi Magaji Najeriya
Kotu A Abuja Tabawa Goodluck Jonathan Daman Tsayawa Takara Afrika
Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • NLC Ta Yabawa Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya Najeriya
  • Uefa Ta Zabi Artan, Ya Jagoranci Wasan Cin Kofin Uefa Super Cup Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NYSC – Sai An Gabatar Da Takardar NERD Kafin Shiga Bautar Ƙasa Afrika
  • Hukumar Hakar Ma’adanai A Kasar Zambiya Ta Dakatar Da Ayyukanta Kimiya
  • Kungiyar Miyetti Allah Ta Bukaci Mambobinta Su Marawa Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna Baya A Gombe Afrika
  • Ana Zargin Tsohon Shugaban Kasar Philippines Da Ta’addaci A Lokacin Mulkinsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Kasar Ghana Ya Soki Manufofin Gwamnatin Amurka Afrika
  • FIFA Ta Yi Wa Malaysia Kaca-kaca Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.