Shugaban Senegal Bassirou Faye ya amince da dokar data ninka shekarun da za’a yanke wa wadanda aka kama da laifin luwadi ko madugo zuwa shekaru 10, kuma ya haramta duk wani mataki na tallata harkar luwadi, yanzu dokar ta fara aiki kamar yadda wata sanarwar gwamnati ta fada.
Wakilan majalisar dokokin kasar da gagarumar rinjaye suka amince da dokar a farkon watan nan, amma shugaban kasar ya fuskanci matsin lamba daga kungiyoyin kasa da kasa masu rajin kare hakkin bil’adama da kada ya sa hannu kan dokar.


